Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar yaki da COVID-19 ta kamfanin CRCC na kasar Sin ta isa Abuja
2020-04-09 13:44:50        cri

Jiya Laraba, a karkashin jagorancin kamfanin CCECC na kasar Sin, tawagar yakar cutar numfashi ta COVID-19 ta kamfanin CRCC na kasar ta isa Abuja, hedkwatar kasar Najeriya, tare da wasu kayayyakin tallafi na gaggawa. Jakadan kasar Sin dake Najeriya Zhou Pingjian, da wakilin gwamnatin tarayyar Najeriya kuma ministan lafiyar kasar Osagie Ehanire su ne suka tarbi tawagar a filin jiragen saman kasa da kasa na Abuja.

A cikin jawabinsa, Jakada Zhou ya bayyana cewa, a wannan ranar ce aka bude birnin Wuhan na kasar Sin. Gaskiya kasar ta samu muhimmiyar nasara wajen yakar cutar. A waje daya kuma, har yanzu ana daukar muhimman matakan da suka dace a fannonin hana dawowar annobar a cikin gida da hana shigo da ita daga waje. A wannan lokaci, ayyukan da kamfanin CRCC ya yi na aikewa da tawagar yakar cutar zuwa kasar Najeriya da kuma kara samar da kayayyakin gaggawa na kiwon lafiya, sun nuna dabarar "cimma muradu da kuma martaba ka'idoji" da kuma manufar "kulla dangantaka da kasashen Afrika bisa gaskiya da kauna da yarda da aminci" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar.

A nasa bangaren, a madadin gwamnatin tarayyar Najeriya, Minista Osagie Ehanire ya yi tawagar maraba da zuwa kasarsa, ya kuma taya gwamnati da jama'ar kasar Sin murnar cimma nasara a kan yakar cutar COVID-19. Ya ce, jama'ar kasar Sin sun samu managartan fasahohi na dalike cutar, zuwan kwararrun bangaren Sin a Najeriya ya karfafa imanin kasar na tinkarar annobar mai sarkakiya. Likitoci da nasa-nasa na kasar Najeriya za su koyi fasahohi daga ma'aikatan lafiyar bangaren Sin, don yaki da cutar yadda ya kamata. Ko da yake har yanzu kasar Sin na fuskantar kalubale sakamakon cutar, amma kamfanonin kasar dake Najeriya suna martaba ra'ayin jin kai don biyan bukatun al'umma, inda suka kawo karin kayayyakin aikin jinya daga kasar ta Sin, hakan ya taimaka wajen warware matsalar rashin kayayyakin dalike cutar da Najeriya ke fuskanta, wannan abun burgewa ne. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China