Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban kamfanin mai da iskar gas na kasar Sin na kokarin gudanar da harkokinsa a kasashen yammacin Afirka
2020-04-07 12:28:29        cri


Cutar numfashi ta COVID-19 na ci gaba da bazuwa a kasashen Afirka daban-daban. Tun farkon bullar cutar, wasu kamfanonin kasar Sin dake kasashen Afirka suka fara daukar wasu managartan matakan kandagarkin yaduwar cutar, a yayin da suke kokarin tabbatar da gudanar da ayyukan kere-kerensu yadda ya kamata. Kamfanin PetroChina International mai kula da harkokin kasashen yammacin Afirka dake karkashin babban kamfanin mai da iskar gas na kasar Sin na daya daga cikinsu.

A halin yanzu, kamfanin PetroChina International mai kula da harkokin kasashen yammacin Afirka na da rassan zuba jari 8 a wasu kasashe 6, ciki har da tarayyar Najeriya, Jamhuriyar Nijar da kuma Chadi, kuma adadin ma'aikatansa ya tasam ma dubu hudu gaba daya. A Jamhuriyar Nijar, kamfanin ya gina filin hakar man fetur mai samar da mai ton miliyan 1 a kowace shekara, da babbar matatar mai mai samar da man fetur ton miliyan 1 a kowace shekara, abun da ya taimakawa kasar wajen habaka masana'antun man fetur da iskar gas. A Chadi ma, kamfanin ya gina filin hakar man fetur mai samar da mai ton miliyan 5 a kowace shekara, da babbar matatar mai mai samar da man fetur ton miliyan 1 a kowace shekara, al'amarin da ya biya bukatun kasar a fannin man fetur da iskar gas.

A nasa bangaren, shugaban rukunin daidaita harkokin babban kamfanin mai da iskar gas na kasar Sin reshen yammacin Afirka, kana babban manajan kamfanin PetroChina International mai kula da harkokin kasashen yammacin Afirka, Wang Junren, ya bayyana cewa, tun bayan barkewar cutar COVID-19, kamfaninsa ya dauki matakan kandagarki ba tare da wani jinkiri ba, inda ya jaddada cewa:

"Kwanakin baya na ziyarci ministan harkokin kasa na Chadi, wanda kuma shi ne babban sakatare a fadar shugaban kasar, inda na gabatar masa da rahoton aiki kan yadda kamfaninmu ke nuna himma da kwazo wajen dakile yaduwar cutar COVID-19 a yammacin Afirka, musamman a Chadi. Ministan ya godewa gudummawar da kasar Sin ta bayar a fannin hana yaduwar cutar a duk fadin duniya, kana kuma a madadin shugaban Chadi Idriss Deby, ya sake nuna goyon-baya ga gwamnatin kasar Sin wajen dakile annobar cutar, ya kuma jinjinawa ayyukan da kamfaninmu ke yi, inda a cewarsa, ayyukan da muke yi a Chadi sun kwantar da hankalinsa sosai."

A halin yanzu, akwai sauran rina a kaba dangane da hana yaduwar cutar COVID-19 a duk fadin duniya. Wang Junren ya ce, tun daga ranar 12 ga watan Maris, kamfaninsa ya soma bukatar ma'aikatansa dukka su yi taka-tsantsan domin daukar duk wani matakin da ya wajaba na kare kansu daga kamuwa da cutar. Game da wasu yankunan da aka riga aka samu bullar wannan cuta, kamfanin ya kara daukar kwararan matakai domin hana yaduwarta a cikin wuraren aiki da gidajen kwanan ma'aikata. Mista Wang Junren ya ce:

"Tun bayan barkewar cutar, zuwa yanzu, kamfaninmu mai kula da harkokin yammacin Afirka na gudanar da ayyukan kere-kere yadda ya kamata, har ma yawan gurbataccen man da muka hako daga wasu manyan filayen mai biyu ya zarce hasashen da muka yi. Haka kuma matatun mai guda biyu suna ayyukan tace mai yadda ya kamata, domin ba da tabbacin samar da isasshen mai ga Jamhuriyar Nijar da Chadi. Ga alama, cutar numfashi ta COVID-19 ba ta yi babbar illa ga ayyukan kere-keren kamfaninmu ba, kana muna gudanar da ayyukanmu daidai bisa burin da muka tsara a farkon shekarar da muke ciki."(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China