Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Italiya: ba za a iya jure wahala ba sai an hada kai tare
2020-04-03 13:15:12        cri

Jiya Alhamis, jaridar Corriere della Sera ta kasar Italiya, ta wallafi wani bayani na masanin ilmin aikin kira na kasar Italiya wato Carlo Rovelli, wanda a cikin sa yake cewa, annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta ilmantar da 'yan Adam cewa, a kauracewa nuna girman kai. Kana barkewar annobar ba kuskuren wani ba ne. Har ila yau ba za a iya daidaita wannan kalubale da 'yan Adam suke fuskanta yadda ya kamata ba, har sai an hada kai sosai.

A ganin masanin, ji da kai da kasashen yammacin duniya suka nuna, ya haifar musu babban kalubale. Kasashen Cuba, Sin, Rasha, har da Albania sun tura likitoci da taimako zuwa Italiya, duk da cewa su ne wadanda aka rika suka a baya.

Ban da haka kuma, ina dalilin da ya sa kasashen Koriya ta Kudu, da Singapore suke yaki da annobar yadda ya kamata, inda kuma mutane kalilan suka rasa rayukansu sakamakon annobar? Me ya sa hakan bai faru a kasashen yammacin duniya ba?

Alamu dai na nuna cewa mai yiwuwa, lokaci zai yi da za a tuna sosai, da irin ji da kai da kasashen yammacin duniya suka nuna. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China