Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNICEF ta jinjinawa Sin saboda tallafawa sashen kiwon lafiyar mata masu jego a Afirka
2020-04-03 10:41:11        cri
Asusun yara na MDD ko UNICEF a takaice, ya jinjinawa kasar Sin bisa kokarinta, na tallafawa ayyukan inganta kiwon lafiyar mata masu haihuwa, da jarirai sabbin haihuwa a kasar Habasha, da ma sauran sassan nahiyar Afirka.

Wata sanarwa da asusun UNICEF ya fitar a jiya Alhamis, ta ce karkashin shirin ta na ba da tallafi, hukumar samar da ci gaban kasa da kasa ta Sin ko CIDCA a takaice, ta raba dalar Amurka miliyan daya, domin tallafawa ayyukan inganta kiwon lafiyar jarirai a Habasha.

Sanarwar ta kara da cewa, wannan tallafi da Habasha ta samu, bangare ne na agajin kudade da yawan su ya kai dala miliyan 8 da CIDCA ta tanada, domin agazawa kasashen Afirka 8, a fannin kiwon lafiyar mata masu jego da jarirai. Ana sa ran wannan tallafi zai ba da damar tsarin kiwon lafiya ga jarirai sabbin haihuwa, ta hanyar karfafa kwarewar jami'an lafiya, da samar da kayayyakin aiki da ake bukata a wannan fanni.

Kaza lika tallafin zai inganta harkokin ba da hidima, na inganta lafiyar jarirai dake bukatar tallafin gaggawa na lafiya, da samar da hadadden tsarin jinya ga jarirai sabbin haihuwa, da cututtukan yara kanana, da samar da kyakkyawan misali na managarcin tsarin aikin jinya.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China