2020-04-07 14:52:52 cri |
Ranar 1 ga watan Afrilu, "rana ce ta kare tsuntsaye ta kasa da kasa", a gabannin ranar, wasu tsuntsayen dake da zama a yankin teku na birnin Shenzhen, sun shiga "takardar muhimman fadamun da za a bada kariya a shekarar 2020" da gwamnatin kasar Sin ta tsara. Yau fiye da shekaru 20 da suka gabata, a wani sansanin sojin ko ta kwana da aka jibge a birnin, an kafa wata tawagar tsaron tsuntsaye, wato a lokacin da sojojin ko ta kwana suke sauke nauyin tsaron kan iyakar kasa da kasa a birnin, suna kuma kokarin tsaron tsuntsaye a yankin. (Sanusi Chen)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China