Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta taka rawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya
2020-04-01 13:13:02        cri


Adadin kididdigar hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO ya nuna cewa, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da annobar cutar numfashi ta COVID-19 ya zarce dubu 700 a kasashe da yankuna fiye da 200, yayin da wasu dubu 33 suka rasa rayukansu. Yaduwar annobar ta kawo mummunar illa ga tattalin arzikin duniya. Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya kiyasta cewa, a shekarar bana, karuwar tattalin arzikin duniya za ta yi kasa da kaso 2.9 cikin dari akan na shekarar 2019. Haka kuma António Guterres, babban sakataren MDD ya nuna cewa, kusan tabbas ne tattalin arzikin duniya zai samu koma-baya, kuma watakila ba a taba ganin irinsa a baya ba. A daidai wannan lokaci, kasar Sin wadda ke kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan 'yan Adam, tana yaki da annobar a gida, tare da karfafa ma'aikata su koma bakin aiki da farfado da masana'antu, a kokarin farfado da tattalin arzikin duniya, wanda annobar ta dakatar da shi.

Yanzu haka sakamakon aiwatar da wasu managartan manufofi da matakai, an gaggauta farfado da zaman rayuwa da komawa bakin aiki. Bai Ming, mataimakin shugaban cibiyar nazarin kasuwannin duniya a ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin, babbar kasa ce wajen kera kayayyaki. Komawa bakin aiki da farfado da masana'antu suna sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki. Haka kuma, kasar Sin, wani muhimmin mataki ne cikin tsarin masana'antun duniya da kuma tsarin samar da kaya na duniya. Yana hada sassa daban daban tare. Alal misali, kasar Sin tana samar wa masana'antun kera motoci na kasa da kasa sassan motoci, yayin da take sayen kananan na'urorin lantarki daga kasashen waje. Komawar ma'aikata bakin aiki da farfado da masana'antun kasar Sin sun samar da kyakkyawar dama ga sauran kasashe ta fannonin guraben aikin yi da raya tattalin arziki.

A halin yanzu ana samun babban sauyi a gida da wajen kasar Sin a fannonin yaki da annobar da kuma bunkasar tattalin arziki. Xu Hongcai, mataimakin darektan kwamitin nazarin manufofin tattalin arizki na cibiyar nazarin kimiyyar manufofin kasar Sin ya yi bayanin cewa, yanzu kasar Sin ta samu ci gaba wajen yaki da annobar, inda ta gaggauta farfado da tsarin samar da kaya da tsarin masana'antu. Amma yaduwar annobar ta yi kamari a kasashen ketare, lamarin da ya sa aka samu bambancin lokaci a tsakanin kasar Sin da kasashen waje. Yanzu kasar Sin tana mai da hankali kan yaki da sake yaduwar annobar a gida da kuma yin kandagarki da dakile shigowar annobar daga ketare. Kasar Sin tana ci gaba da yaki da annobar, tare da farfado da ayyuka, da habaka bukatun da ake da su a gida, a kokarin mayar da asarar da aka yi wajen sayar da kaya zuwa ketare sakamakon yaduwar annobar a sassa daban daban a duniya.

Wang Jun, babban masanin ilmin tattalin arziki a bankin Zhongyuan kuma mamban kwamitin masana na cibiyar kula da mu'amalar kasa da kasa ta fuskar tattalin arizki ta kasar Sin, ya yi karin bayanin cewa, a matsayinta na kasa mafi girma a duniya wajen kera kayayyaki, kasar Sin, wani muhimmin bangare ne na tsarin samar da kaya a duniya. Kana kuma ba za a iya maye gurbinta cikin sana'ar kera kaya ta duniya da kuma tsarin masana'antun duniya ba. Don haka komawar ma'aikata bakin aiki da kuma farfado da masana'antu a kasar Sin sun yi babban tasiri a duniya. Farfado da tsarin samar da kaya na kasar Sin zai amfana wajen tabbatar da tsarin samar da kaya na duniya. Yadda masana'antun kasar Sin suka koma bakin aiki ya yi kama da farfado da tattalin arzikin duniya, sa'an nan ya amfana wajen fitar da tattalin arzikin duniya daga koma-baya.

A ranar 27 ga watan Maris, taron hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na JKS ya jaddada cewa, wajibi ne a inganta hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen waje ta fuskar tattalin arziki da ciniki, da gaggauta kafa tsarin jigilar kaya da samar da kaya na kasa kasa kasa, a kokarin tabbatar da yin jigilar kayayyaki a tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata. Haka zalika a ranar 28 ga watan Maris da safe, jirgin kasa mai dakon kaya na farko, tsakanin kasar Sin da kasashen Turai ya tashi daga Wuhan na lardin Hubei bayan da annobar ta COVID-19 ta barke a birnin. An kiyasta cewa, jirgin zai isa Duisburg na kasar Jamsu bayan kwanaki 15. Wannan ya alamta cewa, an maido da zirga-zirgar jiragen kasa masu dakon kaya tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, wanda hakan ke da matukar muhimmanci wajen tabbatar dayin jigilar kaya tsakanin kasa da kasa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China