Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Malamar da ta gane ma idonta sauye-sauyen da suka faru a Xizang a sama da shekaru dari da suka wuce
2020-04-01 09:16:24        cri

 

 

 

 

 

 

Malama Suolang Drolma ke nan mai shekaru 109 a duniya, wadda take rayuwa a kauyen Reguo da ke birnin Shannan na jihar Xizang ta kasar Sin.Kasancewarta daya daga cikin mutanen da suka fi tsawon rai a jihar, malamar ta gane ma idonta sauye-sauyen da suka faru a jihar cikin shekaru sama da dari da suka wuce.Iyayenta bayi manoma ne, don haka, ita ma ta zama baiwa bayan an haife ta. Iyayenta da yayanta duk sun mutu a sakamakon ayyuka masu wahala da uban gidansu ya tilasta musu yi,a lokacin da ta kai shekaru 47 da haihuwa. Abin farin ciki shi ne, gyare-gyaren dimokuradiyya da aka gudanar a shekarar 1959 a jihar sun kawo karshen tsarin bayi. Daga nan kuma, malama Suolang Drolma ta samu 'yanci, aka kuma ba ta gonaki da gidaje da shanu da tumaki. Daga baya, rayuwarta da iyalanta ta yi ta inganta bisa hazakar aikinsu,suna noman hatsi da dangin gyada, kudin shigar su ya kai yuan dubu 100 a kowace shekara. Sun kuma sayi mota da kuma fadada gidansu.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China