Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamata ya yi wasu 'yan siyasar Amurka su mai da hankali kan karuwar wadanda suka kamu da cutar COVID-19
2020-03-28 15:40:28        cri

Ya zuwa yanzu, kasar Amurka ta riga ta kasance wadda ta fi yawan masu fama da cutar numfashi ta COVID-19 a duniya, kuma a ko wace rana ana samun karuwar wadanda ke kamuwa da cutar. Amma, duk da haka wasu 'yan siyasar kasar suna ci gaba da nuna kiyayya da shafa wa kasar Sin bakin fenti, a maimakon kulawa da ayyukan kandagarki da shawo kan cutar a kasarsu.

A ranar 26 ga wata, sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya sake amfani da kalmar "Cutar Wuhan" a shafinsa na dandalin sada zumunta. A matsayinsa na babban jami'in diplomasiyyar Amurka, kuma a yayin da kasarsa ke cikin mawuyacin hali na yakar annobar, Mike Pompeo, ya gaza mai da hankali kan karfafa hadin kan kasa da kasa wajen yaki da cutar, da warware matsalar rashin kayayyakin kiwon lafiya da kasarsa ke fuskanta, maimakon haka, sai yake tayar da rikicin siyasa. Hakika, mutuncinsa ya zube a idon jama'ar kasar.

A nasa bangaren, a daren ranar 25 ga wata, Peter Navarro, daraktan kwamitin cinikayya na fadar White House, ya kara sanar da cewa, zai kalubalanci shugaban kasar don sanya hannu kan umurnin "sayen kayayyaki kirar Amurka". Kamfanin Reuters ya yi nazarin cewa, burin Peter Navarro shi ne, rage matsayin dogaron da Amurka ke yi kan shigar da magunguna da sauran kayayyakin kiwon lafiya daga kasar Sin.

Abun lura a nan shi ne, a cikin sanarwar taron kolin musamman na G20 na yakar cutar COVID-19 da aka zartas a ranar 26 ga wata, an ce, yanzu an fi bukatar hadin kan kasa da kasa wajen tinkarar cutar.

Baya ga haka, a yayin zantawa ta wayar tarho da aka yi tsakaninsa da takwaransa na Amurka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, hadin gwiwa hanya ce daya kacal da ta dace a tsakanin kasashen biyu. Shugaba Donald Trump shi ma ya bayyana cewa, shi kansa zai kula da wannan aiki, don kawar da cikas da kuma hada kai tsakanin kasashen biyu wajen tinkarar annobar.

Don haka, kamata ya yi wadancan 'yan siyasar Amurka, su gane cewa, ra'ayin yakin cacar baka da nuna kiyayya ba zai taimaka wajen yakar cutar ba. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China