Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin Magaji Ba Ya Hana Na Magajiya
2020-03-27 17:02:35        cri

Yanzu haka dai hankalin duniya baki daya ya karkata kan cutar COVID-19, annobar da yanzu haka masana suka ce, ta harba mutane fiye da dubu 520 a duniya baki daya tare da hallaka mutane fiye da dubu 23. Yayin da kasashen duniya kamar kasar Sin da ta fatattaki wannan annoba, take kuma raba fasahohi da dabarun da ta yi amfani da su ga sauran kasashen duniya ciki har na nahiyar Afirka wajen ganin bayan cuta. A hannu guda kuma, wasu kasashe na kokarin mayar da hannun agogon baya, ta hanyar alakanta cutar da sunan wata kasa da ma furta kalamai na nuna wariya na tsangwama kan wasu daidaikun mutane da sunan COVID-19.

Sanin kowa ne cewa, annoba, babban makiyin daukacin bil-Adam ne, kuma babu wanda yake ganinta, tana kuma ci gaba da bazuwa kamar wutar daji, da ma lakume rayukan jama'a da haddasa barna ba sani ba sabo. Amma, idan har muka bari, wannan matsala ta raba kan al'ummominmu, da alamun wannan na iya zama bala'i mafi muni da annobar COVID-19 din za ta haifarwa duniyarmu. Amma wanda bai ji gari ba, zai ji hoho.

Wannan annoba kusan ta dakatar dukkan harkoki a duniya, kama daga wasanni, muhimman taruka har da harkokin Ibada. Yayin taron G20 da aka kira ta kafar bidiyo a ranar Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a dauki dukkanin matakan yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a duniya baki daya, yana mai cewa, abu mai muhimmanci ga kasashen duniya, shi ne karfafa kwarin gwiwa, da hada kai, da yin aiki tare, domin dakile wannan annoba cikin hadin gwiwa. Da ma masu iya magana na cewa, hannu daya ba ya daukar jinka.

Duk da cewa kasar Sin ta yi nasarar ganin bayan wannan annoba, ta kuma yi alkawarin kara samar da magunguna, da kayayyakin masarufi, da na kandagarkin cutar ga kasuwannin duniya, za ta kuma ci gaba da yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare, da kyautata yanayin kasuwanci a kasar, da habaka shigowa da kayayyaki daga ketare, don ba da gudummawarta ga kiyaye tattalin arzikin duniya.

A saboda haka ne, Xi ya yi kira ga kasashen G20 da su dauki matakai na bai daya, su rage kudin kwastan, da kawar da shingayen cinikayya, don farfado da tattalin arzikin duniya. Da ma an ce, sai an zubar da ruwa a kasa, kafin a taka damshi.

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta nahiyar Afirka ko CDC a takaice, ta ce ya zuwa yanzu haka, adadin mutanen da cutar numfashi ta COVID-19 ta hallaka a nahiyar Afirka sun kai sama da mutum 70, yayin da cutar ta harbi mutane sama da 2,746 a kasashen nahiyar 46.

Kasashen nahiyar da annobar ta fi kamari, sun hada da Afirka ta Kudu mai mutane sama da 700, da Masar mai mutum 456, da Algeria mai 302, sai kuma kasar Morocco mai mutane 225.

Cikin jimillar wadanda cutar ta harba a nahiyar Afirka, cibiyar ta CDC ta ce akwai mutane sama da 200, daga kasashe 14 da tuni suka warke bayan samun kulawar jami'an lafiya. Wannan ne ma ya sa kasar Sin, babbar abokiyar nahiyar Afirka ta kai mata taimako na dabaru da kayayyakin kiwon lafiya da suke kunshe da abin rufe baki da hanci da na gwajin cutar da makamantansu. Wannan ya tabbatar da karin maganar dake cewa, da abokin daka ake shan gari.

Shi ma hamshakin dan kasuwar nan na kasar Sin Jack Ma, ya aikawa kasashen nahiyar Afirka kayayyakin yaki da wannan annoba, ciki har da kasar Najeriya. Wadannan gudummawa da kasar Sin da Jack Ma suka samarwa kasashen nahiyar Afirka, ya kara tabbatar da zumunci na hakika dake tsakanin sannan biyu, sabanin yadda wasu kasashen yammacin duniya ke kokarin yiwa wannan alaka bahaguwar fahimta da ma kokarin bata alaka tsakanin Sin da sauran kasashen duniya. Kamar yadda suke cewa, wai kasar Sin tana gindaya sharudda a taimakon yaki da COVID-19 da take bayarwa. Amma idan mai fadar magana wawa ne, majiyinta ba wawa ba ne. Kuma ruwan da ta daki mutum shi ne ruwa. Ma'ana wanda ya taimake ka a lokacin da kake cikin bukata, ai shi ne masoyinka.

Yanzu dai, ya kamata duniya ta yi tsam ta kuma kalli irin halin da ake ciki, biyo bayan barkewar wannan annaba, da ma tsaikon da ta haifar, ta yadda za a gudu tare a tsira tare. Kukan kurciya aka ce jawabi ne, amma mai hankali ne kadai yake gane wa. Idan kunne ya ji, aka ce gangan jiki ya tsira. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China