Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cutar ta kawo babbar illa ga gasannin wasan motsa jiki sosai a duniya
2020-03-26 15:14:53        cri

Cutar ta kawo babbar illa ga gasannin wasan motsa jiki sosai a duniya, a wannan rana, an kuma sanar da soke gasanni da dama, daga cikin su kuwa hadda babban taron wasan motsa jiki na shekarar 2020 da aka sa ran aiwatar da shi a watan Afrilu mai zuwa a birnin Beijing, wanda kwanan baya aka canja wurin aiwatarwa a Lausanne na Switzerland, amma a karshe an soke shi. Ban da wannan kuma, ma'aikatan hedkwatar kwamitin shirya gasar wasan motsa jiki na Olympics ta kasa da kasa, sun fara aiki a cikin gida daga yau Litinin. 

FIFA ta amince da jinkirta lokcin gasar kwallon kafa ta Turai da kuma ta nahiyar Amurka

Jiya Talata an sanar da jinkirta lokacin gasar kwallon kafa ta Turai da kuma ta nahiyar Amurka bi da bi, zuwa watan Yuni da Yuli na shekarar 2021, a sakamakon barkewar cutar COVID 19 a duniya. Da safiyar yau agogon birnin Beijing, shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasa da kasa FIFA Gianni Infantino ya ba da sanarwa, inda ya bayyana amincewa da wadannan sauye sauye, haka kuma ya ba da shawarar dage lokacin gasar kwallon kafa ta kungiyoyin FIFA da aka shirya yi a shekarar 2021. Ban da wannan kuma, a cewarsa, za a tattauna kan ko yaushe ne za a gudanar da gasar ko a karshen rabin shekarar 2021 ko a shekarar 2022 ko kuma ta 2023, a lokacin da aka kara samun tabbas kan halin da ake ciki. Ya ce, zai yi musanyar ra'ayi sosai da gwamnatin kasar Sin da kuma kungiyar kwallon kafa ta kasar don kawar da mumunan tasiri bisa iyakacin kokari. (Amina Xu)

Kashi 35 Na 'Yan Wasan Valencia Sun Kamu Da Coronavirus

Kungiyar kwallon kafa ta Valencia dake kasar Sipaniya ta bayyana cewa kashi 35% cikin 100 na 'yan wasa da ma'aikatan kungiyar sun kamu da cutar Coronabirus sakamakon yadda cutar take ci gaba da yaduwa a duniya. Kungiyar kwallon kafa ta Balencia, wadda take buga gasar rukuni-rukuni ta kasar Sipaniya ta buga wasa da kungiyar Atlanta dake kasar Italiya a ranar 19 ga watan February dalilin daya sa ake ganin a wannan lokacin ne suka kamu da cutar saboda daman 'yan kasar Italiya sunfi kamuwa da cutar musamman a nahiyar turai. Bayan da aka ci gaba da samun alamu da tsoro a zukatan shugabanni da masu koyarwa da 'yan wasan kungiyar ne sai aka bawa kowa umarni da yaje domin a gwada lafiyarsa kuma a haka ne aka gano halin da kungiyar take ciki. A ranar Litinin ne kungiyar ta ce 'yan wasan kungiyar da suka kamu da cutar tun farko suna ci gaba da murmurewa ya yin da ake ba su kulawar da ta dace kuma babu wata damuwa a tattare dasu sannan kuma kungiyar ta bayyana cewa tana daukar dukkan matakan kariya domin kula da wadanda basu dauka ba. Dan wasan bayan kungiyar kuma dan kasar Argentina, Ezekuiel Garay ne dan wasa na farko a La Liga da ya bayar da sanarwar kamuwa da cutar a ranar Lahadin data gabata sai dai daga baya an sake gano wasu daga cikin 'yan wasan cikin har da Elekuim Mangala. Valencia tana mataki na bakwai akan teburin laligar bana kuma tayi rashin nasara a gasar kofin zakarun turai zagaye na 16 da kungiyar Atlanta ta doke ta daci 8-4 a gaba daya wasanni biyun sai dai tun a ranar Alhamis din data gabata ne aka dakatar da gasar ta La Liga bayan killace tawagar Real Madrid kuma kasar Spaniya ce kasa ta biyu da cutar ta fi kamari a Nahiyar Turai bayan Italiya kuma tana kokarin saka dokar-ta-baci ranar Litinin.

Ministan Wasannin Italiya Ya Soki Shugabannin Gasar Siriya A

Ministan wasanni na Italiya ya tuhumi manajojin gasar Siria A da kasancewa masu taurin kai bayan sun yi watsi da kiran da yayi na dakatar da gasar saboda coronabirus wadda ta addabi dubunnan mutane a kasar. Tun da farko, Vincenzo Spadafora ya ce hankali ma ba zai dauka ba idan aka ci gaba da buga wasannin kwallon kafa bayan da aka killace mutum miliyan 16 a kasar ta Italiya sai dai amma an ci gaba da buga wasannin a karkashin gasar ta Siriya A a ranar Lahadi, duk da cewa babu dan kallon da aka bari ya shiga cikin filin wasan. Minista Spadafora ya ce duniyar kwallon kafa na ganin ta fi karfin dokoki da sadaukar da kai saboda haka matakin da hukumar kula da gasar ta dauka na ci gaba da buga wasannin na Siriya A abin takaici ne. Ya yin da yake hira da tashar talabijin mallakin gwamnati ta RAI, ya kara da cewa a ranar Lahadi an buga wasanni saboda taurin kan Gasar Siriya A da shugabanta Paolo dal Pino saboda haka yana bawa 'yan Italiya shawara da su zauna a gidajensu. A makon jiya, gwamnatin Italiya ta sanar da cewa za'a rika buga dukkan wasannin a cikin filayen wasan da babu 'yan kallo cikinsu sam-sam har zuwa ranar 3 ga Afrilu kuma an buga wasannin kamar na Parma da SPAL sai dai wasan an fara shi ne bayan jinkirin minti 75, kuma bayan da Spadafora ya mika umarnin nasa. An kuma buga wasu wasanni hudu ba tare da 'yan kallo sun shiga filayen wasannin ba cikinsu Jubentus ta buga da Inter Milan sannan ana kuma Sassuolo ta buga wasa tare da kungiyar Brescia ranar Litinin duk da halin da ake ciki. Kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta Italiya, AIC ta fitar da wata sanarwa bayan da aka kammala wasan Parma da SPAL, wanda a cikinta ta soki matakin ci gaba da buga wasannin na Lahadi amma a nasu bangaren masu kula da gasar kwallon kafa a kasar, Lega Serie A sun ce tun farko sun bi tsarin da aka amince da shi ne na hana 'yan kallo shiga filayen wasa. Sanarwar ta kuma soki hukumomin kasar da kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta Italiya da yin katsalandan gabanin wasan da aka buga tsakanin Parma da SPAL wanda kungiyar ta bayyana halin da ake ciki a matsayin abin tsoro.

Chelsea Ta Hakura Da Timo Werner Ta Koma Neman Dembele

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta hakura da zawarcin da take yiwa dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig, inda a yanzu ta mayar da hankalinta wajen zawarcin dan wasan Lyon, Moussa Dembele Dembele, mai shekara 23 a duniya dai yana daya daga cikin 'yan wasan gaba a gasar firimiya da tauraruwarsu take haskawa kuma kungiyoyin firimiya da suka hada da Manchester United da Chelsea ne suke zawarcinsa. Kamar yadda rahotanni daga kasar Faransa suka bayyana Chelsea ta hakura da ci gaba da zawarcin dan wasa Timo Werner wanda kungiyar kwallon kafa ta Liberpool take zawarci kuma shima dan wasan yafi kaunar zuwa Liberpool din. Tun a watan Janairu kociyan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea yaso kungiyar ta sayo masa dan wasan gaba wanda zai zama kishiya ga Tommy Abraham wanda yake fama da ciwo sannan Olivier Giroud bashi da tabbacin zaman kungiyar duk da haka. Sai dai a kwanakin baya kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United yaje har kasar Faransa yaga dan wasan kuma shima yana son sayan dan wasan gaba mai zura kwallo a raga wanda hakan yake nufin Chelsea za ta samu kalubale daga United. Moussa Dembele dai, wanda ya buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Celtis ta kasar Scotland da Fulham ta Ingila ya zura kwallaye 16 cikin wasanni 27 daya buga a kungiyar kwallon kafa ta Lyon a kasar Faransa.(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China