Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ce ta fara tsokano batun asalin cutar COVID-19
2020-03-24 20:53:14        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce har yanzu sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, na ambatar cutar numfashi ta COVID-19 da sunan "Cutar Wuhan " ta kafofin sadarwa, duk kuwa da nanata rashin amincewa da hakan, da Sin ta jima tana yi.

Geng Shuang, wanda ya yi wannan tsokacin ya kara da cewa, Amurka ta ci gaba da ambaton wannan cuta da cutar kasar Sin, tana mai kokarin shafawa Sin din bakin fenti. Ya ce tabbas al'ummar Sinawa sun yi tir da wannan mataki, suna kuma matukar adawa da shi.

Jami'in ya ce Amurka ce ta fara tsokano batun sa-in-sa da sassan biyu ke yi game da asalin wannan cuta. Ita ce kuma ta fara ambatar cewa asalin cutar shi ne kasar Sin, ko kuma kiran cutar da cutar Wuhan.

Tun daga ranar 6 ga watan Maris din nan ne dai Mr. Pompeo ya fara furta kalmar "Cutar Wuhan". Daga nan ne kuma, wasu 'yan siyasa da manyan jami'an gwamnatin Amurka, suka ci gaba da amfani da kalmar domin bata kasar Sin, lamarin da kuma ya yi matukar muzanta kasar Sin, kana al'ummar Sinawa suka yi matukar Allah wadai da shi.

Daga karshe Geng Shuang, ya jaddada burin kasar Sin, na ganin Amurka ta saurari kalamai masu fa'ida daga sassan duniya, ta kuma dakatar da yada kalamai da ba su dace ba game da kasar ta Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China