Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya na daukar matakan hana yaduwar cutar COVID-19
2020-03-25 09:21:09        cri


A yayin da cutar numfashi ta COVID-19 ke ci gaba da bazuwa a duk fadin duniya, kasashen Afirka daban-daban na fuskantar babbar barazanar yaduwar cutar, ciki har da tarayyar Najeriya, kasa da ta fi yawan al'umma a duk fadin nahiyar Afirka.

To, menene ya kamata mutanen Najeriya su fahimta game da cutar? Yaya za'a yi domin kare kai daga kamuwa da cutar? Ko akwai darussan da Najeriya da ma sauran kasashen Afirka za su iya koya daga kasar Sin, sakamakon dimbin nasarorin da ta cimma wajen ganin bayan annobar cutar?

Game da wadannan batutuwa, wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da wasu masana a bangaren lafiya na Najeriya, domin su tofa albarkacin bakinsu kan matakan da gwamnatin Najeriya ta dauka wajen hana yaduwar cutar COVID-19, da ra'ayinsu kan kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi a wannan fanni.

Wadannan masanan su ne, Dr. Nasiru Sani Gwarzo, kwararren likita a bangaren yaki da cututtuka na al'umma, kana likita mai yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya, da Dr. Imam Wada Bello, babban darakta mai kula da lafiyar al'umma da cututtuka ta ma'aikatar lafiya dake jihar Kano a Najeriya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China