Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan siyasar Amurka ku bar yaudarar al'umma
2020-03-23 20:58:20        cri

A ranar 20 ga watan nan ne jaridar New York Times ta Amurka, ta wallafa wani sharhi mai taken "Kar ku bar Trump ya gudu", inda sharhin ya bayyana matsayi daban daban masu sabawa da juna da shugaban na Amurka ya dauka, game da cutar COVID-19 na baya da kuma na yanzu.

Da farko dai, game da yanayin cutar a kasar, ya nuna halin-ko-in-kula a cikin kusan watanni biyu da suka wuce, sai dai a kwanan baya, ya ce tuni ya tsinkayi inda cutar za ta dosa.

Na biyu kuma game da kokarin da kasar Sin ta yi, ya fara ne da yabawa, kafin daga bisani ya bata sunan kasar, har ma ya rika kiran cutar da suna cutar kasar Sin.

Sakon da sharhin ya isar shi ne, gwamnatin kasar Amurka na neman shafa wa kasar Sin kashin kaji don kawar da hankalin al'umma, ta yadda za ta kai ga ceton kasuwar hannayen jarin kasar. Sai dai jerin al'amuran da suka faru kwanan baya, ciki har da yadda jami'an kasar da dama dake cikin kwamitin leken asiri na majalisar dattawan kasar suka sayar da hannayen jarinsu, da kudinsu ya kai sama da miliyan bisa bayanan sirrin da suka samu, a yayin da suke boye ainihin halin da ake ciki ga al'ummar kasar, suna ta kara jawo fushin al'ummar kasar.

Abin da ya kara ba al'umma takaici shi ne, duk da karancin kayayyakin gwajin cutar, amma sanannun 'yan siyasa da masu hannu da shuni na kasar, sun fi samun fifiko wajen karbar gwajin, duk da cewa ko alamar kamuwa da cutar ba su nuna ba. A game da hakan, shugaban Amurka ya amsa cewa, "watakila haka rayuwa take."

Yanzu dai Amurka ya zamanto daya daga cikin kasashen da cutar ta fi kamari. Kuma bai kamata 'yan siyasar Amurka su ci gaba da yaudarar jama'a ba, a maimakon haka, ya dace su mai da rayukan al'umma a gaban komai, kuma su gaggauta daukar matakan kandagarkin cutar, a maimakon dora laifi kan sauran kasashe. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China