Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rayukan jama'a ko kudi? Ga yadda 'yan siyasan kasar Amurka suka zaba
2020-03-21 20:20:44        cri

Zuwa karfe 11 da dare na ranar 20 ga wata, bisa agogon gabashin kasar Amurka, an riga an samu mutane 19624 da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar. Wannan adadi ya ninka har fiye da sau 1300 cikin makonni 2 da suka wuce.

A daidai wannan rana, wani abu ya fusata Amurkawa sosai, wanda ya sa kalmar "Resign Now", wato "A yi murabus yanzu!" ta zama wadda aka fi neman kallo a shafukan intanet na kasar.

Wanda ya fusata jama'ar Amurka a wannan karo, shi ne mista Richard Burr, shugaban kwamitin aikin leken asiri, kana mamban kwamitin aikin lafiya na majalisar dattawan kasar Amurka.

Dalilin da ya sa ake fushi da shi, shi ne, kafofin watsa labarai na kasar sun gano cewa, ko da yake Richard Burr ya san ainihin yanayin da ake ciki wajen samun barkewar cutar COVID-19 a kasar Amurka, amma ya yi kokarin boye wannan bayani a matsayin sirri. Har ma ya sayar da dimbin hannayen jari duk a cikin sirri.

Asirin da aka boyewa kowa

Gidan rediyon NPR na kasar Amurka ya watsa wata muryar da aka dauka, wadda ta nuna cewa, a ranar 27 ga watan Fabrairun da ya gabata, mista Richard Burr ya taba bayyana wajen wata haduwar abokansa cewa, "saurin yaduwar cutar COVID-19 zai iya wuce na duk wata cutar da aka taba gamuwa da ita a wani tarihi mai kusa", kana "za ta yadu sosai kamar yadda mura ta yi a shekarar 1918".

Murar da ta bullo a shekarar 1918 ta haddasa mutuwar mutane dubu 600 a kasar Amurka. Abin takaici shi ne, wadanda suka yi sa'ar sauraron wannan gargadi, wasu hamshakan masu kamfanoni ne kadai. Wadannan mutane da kamfanoninsu, ko kuma kungiyoyin siyasar su, sun taba ba da kudin da ya zarce dalar Amurka dubu 100 kyauta ga Richard Burr, don taimaka masa yakin zabe a shekarar 2015 da ta 2016.

Yayin da a wani bangare na daban, mista Burr bai ce komai ga jama'ar kasar ba. Maimakon haka, sakon kawai da jama'ar kasar suka ji daga gwamnati shi ne "Babu hadari sosai."

Duk a ranar 27 ga watan Fabrairun, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ci gaba da alkawarta cewa, wai "an samu shawo kan annoba, wadda za ta bace daga doron kasa cikin sauri". Amma zuwa yanzu, adadin wadanda suka harbu da cutar a kasar Amurka ya karu zuwa 19624, daga 15 da aka samu a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Sayar da hannayen jari cikin sirri

Bisa binciken da jaridar New York Times ta kasar Amurka ta yi, an ce Richard Burr ya fara sayar da hannayen jarin da ya mallaka, wasu makwanni kafin a samu babbar faduwar darajar hannayen jari a kasar.

Tarihin musayar jannayen jari na mista Burr ya nuna cewa, a ranar 13 ga watan Fabrairu kadai, ya sayar da hannayen jarinsa har sau 33, inda darajar hannayen jarin da ya sayar ta kasance tsakanin dalar Amurka dubu 628 zuwa miliyan 1.72.

Mista Richard Burr ya shaida mana mene ne "Nuna fuska biyu", inda a wani bangare ya yaudare jama'a da karairayi, yayin da a wani bangare na daban, yake kokarin amfani da wasu damammaki wajen cika aljihunsa.

Masu iya magana kan ce, "Idan an ga kyankyaso cikin wani daki, to, akwai sauran kyankyasai a ciki." Ban da Richard Burr, karin 'yan siyasan kasar Amurka sun fara nuna halayyarsu, yayin da ake fuskantar annobar COVID-19.

Zuwa yanzu, ana zargin a kalla 'yan majalisar dattawa 3 na kasar Amurka da sayar da dimbin hannayen jari kafin a fara ganin alamar matsala a kasuwa. Wadannan 'yan siyasa sun hada da Dianne Feinstein, da James Inhofe, da Kelly Loefler.

Rayukan jama'a ko kudi, wane ya fi muhimmanci?

Yayin da manyan kusoshin kasar Amurka suka fara janye jiki daga kasuwa don kare moriyarsu, jama'ar kasar ba su san abun dake faruwa ba, ko a fannin yanayin yaduwar cutar, ko kuma a fannin tasirinta kan tattalin arziki.

Har zuwa yanzu, jihohin kasar na ci gaba da fuskantar matsala ta fuskar samun kayayyakin aikin jinya, gami da na'urorin gwaje-gwajen kwayoyin cuta. Sai dai yayin da yake tsokaci kan wannan batu, shugaban kasar Amurka ya ce: "Sayen kayayyaki da yawa da kuma jigilarsu zuwa jihohi daban daban ba aikin gwamnatin tarayya ba ne, domin mu ba masu jigilar kayayyaki ba ne."

Ban da haka, game da wadanda za a yi wa gwaje-gwajen kwayoyin cutar COVID-19, ana samar da fifiko ga masu hannu da shuni, maimakon wadanda lafiyar jikinsu ke cikin yanayi mai tsanani a kasar Amurka, kamar yadda jaridar New York Time ta wallafa.

Sa'an nan yayin da shugaba Donald Trump ke tsokaci game da wannan batu, ya amince cewa, attajirai da shahararrun mutane na kasar Amurka sun fi samun kulawa, inda ya kara da cewa, "Zaman rayuwar mutum kamar haka yake."

Ma iya cewa annoba tamkar madubi ne, dake nuna mana munafukin wasu 'yan siyasa, gami da wanda gwamnatin wata kasa ke bautawa. Za a zabi rayukan jama'a ko kuma kudi? Wasu 'yan siyasan kasar Amurka sun riga sun ba da amsa a aikace-aikacensu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China