Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin jarin ketare suna cike da imani kan kasuwar kasar Sin
2020-03-18 10:48:10        cri

Kwanan baya, kungiyar 'yan kasuwan kasar Amurka dake kasar Sin wato AmCham China a takaice, ta fitar da rahoton binciken muhallin kasuwancin kasar Sin na shekarar 2020, inda aka yi nuni da cewa, duk da cewa, yanzu kasar Sin tana fama da annobar cutar numfashi ta COVID-19, amma yawancin kamfanonin Amurka za su kara habaka cinikayyarsu a kasuwar kasar Sin, cikin kamfanonin da aka ziyarta kaso 63 bisa dari sun bayyana cewa, za su kara zuba jari a kasar Sin a shekarar 2020 da muke ciki.

Abu mai faranta rai shi ne, yayin da ake kokarin dakile bazuwar annobar a kasar Sin, kamfanonin da 'yan kasuwar ketare suka zuba suna kara habaka cinikayyarsu a kasar, misali kamfanin Starbucks mai samar da kofi na Amurka, zai gina wani kamfanin gasa waken kofi a birnin Kunshan na lardin Jiangsu na kasar Sin, kamfanin da zai kasance aikin zuba jari mafi girma na Starbucks a ketare.

Yanzu aikin shawo kan annobar a kasar Sin ya samu sakamako bisa mataki na farko, kamfanoni a fadin kasar suna dawowa bakin aiki a kai a kai, kuma tattalin arzikin kasar zai karu yadda ya kamata, kamfanonin ketare su ma suna dawowa bakin aiki cikin sauri, inda mataimakin shugaban rukunin ABB mai samar da lantarki Zhang Zhiqiang ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da tushe mai karfi, rukunin ABB yana cike da imani kan makomar tattalin arzikin kasar Sin. Rahotanni sun nuna cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka wajen dakile annobar sun samu sakamako mai gamsarwa, kana babbar kasuwar kasar Sin tana kara jawo hankalin masu jarin ketare.

Rahoton binciken muhallin kasuwancin kasar Sin na shekarar 2020 na kungiyar 'yan kasuwan kasar Amurka dake kasar Sin shi ma ya nuna cewa, adadin kamfanonin jarin Amurka, wadanda suka dauka cewa muhallin zuba jarin kasar Sin ya kyautata, ya karu da kaso 12 bisa dari. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China