Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a yankin kudu da hamadar Sahara ya zarce 100
2020-03-17 16:54:12        cri

Adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a yankin kudu da hamadar Sahara, ya zarce 100. An samu bullar cutar a kasashe sama da 20, inda kasashen suka daura damarar yaki da ita, cikinsu har da Afrika ta Kudu da Nijeriya da Habasha.

Daga cikin kasashen 20, cutar ta fi kamari a kasar Afrika ta Kudu. An samu bullar cutar na farko a kasar ne a ranar 5 ga wata, kuma ya zuwa jiya Litinin, an tabbatar da mutane 62 sun harbo.

A jiyan ne kuma kasar Liberia ta sanar da samun bullar cutar na farko. Gwamnatin kasar ta ce an tabbatar da wani babban jami'inta da ya yi bulaguro zuwa kasar waje a matsayin mutum na farko da ya kamu cutar numfashi ta COVID-19 a kasar.

Su ma kasashen Tanzania da Benin da Somalia, sun tabbatar da bullar cutar na farko a jiya. Ma'aikatar lafiya ta kasar Benin ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, wanda ya kamu da cutar wani dan kasar Burkina Faso ne da ya shiga kasar a ranar 12 ga wata.

A Tanzania kuwa, hukumomin lafiya na kasar sun ce mai dauke da cutar, wata mata ce da ta bi jirgin RwandaAir daga Belgium, zuwa kasar a ranar Lahadi.

A nata bangaren, gwamnatin Somalia wadda ita ma ta samu bullar cutar a karon farko, ta sanar da dakatar da zirga-zirgar dukkan jiragen kasashen waje na tsawon kwanaki 15, daga gobe Laraba.

Galibin wadanda suka kamu da cutar a wadancan kasashe, mutane ne da suka koma ko suka je yankin, daga nahiyar Turai da arewacin Amurka.

A cewar cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afrika ta Kudu NICD, an samu wadanda suka kamu da cutar a baya-bayan nan a kasar ne a lardunan Gauteng da Kwazulu-Natal da Limpopo da Mpumalanga da Western Cape. Kana dukkan wadanda suka kamu da cutar, sun yi tafiya zuwa kasashen Turai da Amurka da Canada da India ko Hadaddiyar Daular Larabawa.

Daga cikin mutane 62 da suka kamu da cutar a kasar, akwai mutum biyu da suka kamu a cikin kasar, wadanda ake binciken lafiyarsu. Sannan ta na aikin tabbatar da gwaje-gwaje da kuma bibiyar mutane da marasa lafiyan suka yi hulda da su.

Cibiyar ta kara da cewa, la'akari da yadda galibin masu dauke da cutar shigar da ita suka yi daga Turai da arewacin Amurka, kasar ta haramta zuwa kasashen da cutar ta fi kamari.

Shugaban kasar, Cyril Ramaphosa, wanda ya ayyyana cutar a matsayin annobar da ta aukawa kasar, ya ce daga gobe 18 ga wata, an haramta bulaguro zuwa kasashen dake tsananin fama da cutar.

Baya ga haka, shugaba Ramaphosa ya sanar da wasu matakai na gaggawa da kasar ta dauka, wadanda suka hada da rufe makarantu da haramta taron da ya wuce na mutum 100 da tilasta gwaji da kebe kai ga 'yan kasar da suka koma gida daga kasashen dake fama da cutar.

Haka zalika, gwamnati na karfafa sa ido da bincike da gwaji, a tasoshin shiga kasar.

A jiya Litinin ne ma'aikatar kula da yawon bude ido ta kasar, ta ce za ta dage shirin yawon bude ido na Africa Travel Indaba, wanda aka shirya yi daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Mayu, a birnin Durban.

Hari ila yau, an soke wasu bukukuwa da aka shirya yi a cikin wannan watan.

Daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO a nahiyar Afrika, Matshidiso Moeti, ya ce la'akari da yadda hukumar ta ayyana cutar numfashi da kwayar cutar Corona ke haifarwa a matsayin annobar da ta shafi duk duniya, wajibi ne dukkan kasashe su hada hannu wajen ganin bayanta.

Ya zuwa ranar 12 ga wata, WHO ta tura kwararru 62, da suka hada da na bangarorin kula da marasa lafiya da kandagarkin kwayoyin cuta da dakile yaduwarsu da kula da lafiyar al'umma da sauransu, zuwa kasashe 18, kuma za a kara tura wasu kari a nan gaba.

A cewar WHO, wadannan kwararru da suka isa kasashen da aka tabbatar da bullar cutar, na taimakawa gwamnatoci tunkarar cutar, da kokarin dakile yaduwarta da kuma kula da wadanda suka kamu.

Daraktan janar na hukumar kula da lafiya ta kasar Guinea, Sakoba Keita, ya ce akwai bukatar musayar bayanai da dabaru tsakanin kasashen dake yankin. Inda ya yi kira ga kasashen su dauki ingantattun matakai wajen rage tafiye-tafiyen 'yan kasashen dake fama da cutar a nahiyar.

Ya ce game da kudin aiwatar da matakan tunkarar cutar, kowa ya san cewa kasashen Afrika ba su da isassun kudi, amma ana bukatar kyakkyawan kudurin shugabanci, ta yadda kasafin kudin kasa zai iya daukar nauyin magance batun cikin sauri.

Sakoba Keita, ya kuma yabawa kasar Sin bisa matakan da ta dauka na yaki da annobar.

Shi ma a nasa bangaren, Tajuddeen Raji, shugaban sashen kula da cibiyoyin kiwon lafiyar al'umma da bincike na cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC, ya ce cibiyar CDC ta kasar Sin, na aiki kafada-da-kafada da takwararta ta nahiyar Afrika, inda take taimakawa kwamitin ko-ta-kwana da aka kafa a baya-bayan nan domin yaki da cutar COVID-19.

Ya ce akwai Basine wanda kwararren mai ba da shawara ne dake aiki tare da su. Kuma yana shiga ana damawa da shi sosai a cikin kwamitin, inda yake bayar da shawarwarin da suka dace. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China