Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanoni masu jarin waje na cike da imani ga makomar tattalin arzikin kasar Sin
2020-03-15 16:28:01        cri

Wurare daban daban na kasar Sin suna dukufa wajen bada taimako ga kamfanoni masu jarin waje domin warware matsalolin da suka gamu da su a lokacin dawowarsu bakin aiki, matakan da suka dauka sun karfafa aniyar kamfanonin wajen zuba jari a kasar Sin.

Bisa babban goyon baya da gwamnatin kasar Sin ta yi musu, kamfanonin kasar Amurka da kamfanonin kasar Jamus da wasu manyan kamfanoni masu jarin waje dake birnin Shenzhen sun koma bakin aiki, ya zuwa yanzu, dukkanin muhimman kamfanoni masu samun jarin waje sun farfado da ayyukansu.

A birnin Shanghai kuma, tawagogin wakilan gwamnatin birnin sun kai ziyara a hedkwatocin kamfanonin kasa da kasa da kamfanoni masu jarin waje gaba daya guda 720, domin bada taimako gare su wajen warware matsalolin dake gabansu. A halin yanzu kuma, kamfanoni masu samun jarin waje kashi 99.9% sun riga sun koma bakin aiki. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China