Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana kokarin cimma manufar fitar da mutane daga kangin talauci kan lokaci kuma bisa shirin da aka tsara
2020-03-11 14:26:59        cri

Rahotanni daga taron manema labaru da majalisar gudanarwar kasar Sin ta shirya jiya Talata na cewa, yanzu ana gaggauta gudanar da ayyukan yaki da talauci bisa matakai daban daban a wurare daban daban na kasar, inda kuma aka ba da muhimmanci kan maido da ayyukan gona cikin hanzari a wuraren da ke fama da talauci, a kokarin cimma manufar fitar da mutane daga kangin talauci kan lokaci kuma bisa shirin da aka tsara.

Rahotannin sun nuna cewa, kawo yanzu yawan ayyukan yaki da talauci da aka kaddamar da su a larduna 22 da ke tsakiya maso yammacin kasar Sin ya kai kashi 1 cikin kashi 3 bisa jimillar ayyukan, kana kuma, yawan ma'aikatan da suka koma bakin aiki a wuraren tafiyar da ayyukan yaki da talauci ya wuce kashi 60 cikin kashi 100 bisa jimillar ma'aikata a wadannan wurare. Huang Yan, wata jami'ar ofishin kula da ayyukan yaki da talauci na majalisar gudanarwar kasar Sin ta yi bayani da cewa, "Mun samar da kudi na taimakon masana'antun dake aikin yaki da talauci da kuma kamfannoni. Mun kuma kara karfin tallafawa ayyuka masu ruwa da tsaki a matakai daban daban, wadanda annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta fi yi wa illa. Har ila yau muna taimakawa kamfanoni masu karfin yaki da talauci da kuma wuraren aiki, ta fuskar tallafin kudi da rancen kudi, wadanda suka samar da guraben aikin yi ga masu fama da talauci da yawa. Mun bada fifiko kan ayyukan da aka hanzarta gudanar da su don fitar da mutanen daga talauci sakamakon barkewar annobar, da kuma wadanda za su kara kudin shigar masu fama da talauci."

Da zummar taimaka wa masu fama da talauci su maido da ayyukansu, gwamnatin Sin ta aiwatar da manufar ba da gatanci ta fuskar rancen kudi. Su Guoxia, wata jami'a ta daban a ofishin kula da ayyukan yaki da talauci na majalisar gudanarwar kasar Sin ta yi bayani da cewa,"Idan wani ya gaza biyan bashi kan lokaci sakamakon barkewar annobar, za mu tsawaita lokacin biya bashin da rabin shekara, kuma ba za mu sanya sunansa cikin jerin sunayen wadanda ba su biya bashi kan lokaci ba. Sa'an nan kuma mun kara saurin biyan bukatun manoma wadanda suka nemi samun sabon rancen kudi."

Haka zalika, hukumomi masu ruwa da tsaki na kasar Sin sun kafa tsarin taimakawa juna wajen yaki da talauci, a kokarin warware matsalolin yin jigilar iri da takin zamini da maganin kashe kwari masu kawo barna da harawa da sauran kayayyakin da ake bukata a fannin aikin gona a wuraren da ke fama da talauci. Sun kuma jagoranci maido da ayyukan gona cikin sauri, tare da taimakawa sayar da amfanin gona a wuraren da ke fama da talauci. Jami'an ofishin kula da ayyukan yaki da talauci na majalisar gudanarwar kasar Sin sun nuna karfin zuciya wajen rage illar barkewar annobar da cimma manufar fitar da mutane daga kangin talauci kan lokaci kuma bisa shirin da aka tsara. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China