Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakiliyar Sin: A dauki dabarar da ta dace da yanayin kasa a kokarin kare hakkin bil adama
2020-03-11 12:27:02        cri
A jiya Talata, an yi babban muhawara game da batun kare hakkin bil adama yayin taro na 43 na majalissar kare hakkin bil adama ta MDD. Inda Madam Liu Hua, wakiliyar musamman ta ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin game da kare hakkin bil adama, ta yi nuni da cewa, ba dole ne ba sauran kasashe su bi tsarin kasashen yammacin duniya game da kare hakkin dan-Adam, kuma ya kamata kasashe daban daban su bullo da dabarun da suka dace da yanayinsu.

Liu Hua ta kara da cewa, a game da batun Xinjiang na kasar Sin, ana nuna fuskoki biyu a duniya. Daya daga cikin shi ne, wasu kasashen yamma sun ki amsa gayyatar da Sin ta yi musu na su turo tawagoginsu domin su ziyarci jihar Xinjiang, yayin da a sa'i daya suna ta kokarin yada jita-jita gami da shafawa kasar Sin bakin fenti. Sa'an nan daya fuskar ta daban ita ce, sama da kasashe 70 sun ba da cikakken goyon baya ga manufofin Sin a fannin raya jihar Xinjiang, da ci gaban da kasar ta samu a fannin kare hakkin dan Adam, ta hanyar aikewa da wasiku da gabatar da jawabai a wurare daban daban. Wadannan kasashe sun fito ne daga nahiyoyin Asiya, Afirka, Turai, da Amurka. Da yawa daga cikinsu mambobi ne na kungiyar kasashe Musulmai, kuma yawancinsu sun taba tura wakilansu don ziyartar jihar Xinjiang da gane ma idanunsu hakikakin yanayin da ake ciki.

Kasar Sin ta sha nanata cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi amfani da matakai na doka wajen yaki da ta'addanci da kuma kawar da tsattsauran ra'ayi a cikin jihar Xinjiang, gami da kafa cibiyoyin koyar da sana'o'i da ba da horo, wadanda suka daidaita yanayin tsaro sosai a Xinjiang, tare da kiyaye hakkin bil adama na dukkan al'ummomi, da kuma samun goyon baya daga al'ummomi daban daban. A halin yanzu, dukkan wadanda suka halarci horo na kawar da tsattsauran ra'ayi sun gama karatu. Kasar Sin ta bayyana a lokuta da dama cewa, tana fatan karbar babban jami'in kare hakkin dan adam na MDD a ziyarar da zai kawo kasar Sin da jihar Xinjiang a wannan shekarar da muke ciki, in ji Madam Liu Hua. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China