Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan jarin da za a zuba kai tsaye zai ragu a duk fadin duniya, ban da kasar Sin sakamakon barkewar annobar COVID-19
2020-03-09 12:16:02        cri

Wani rahoton nazari da hukumar babban taron cinikayya da neman ci gaba ta MDD, UNCTAD ta bayar a jiya 8 ga wata, ya nuna cewa, yawan jarin da za a zuba kai tsaye zai ragu daga 5% zuwa 15% a duk fadin duniya sakamakon barkewar annobar COVID-19. Ko da yake tabbas hakan zai kawo illa ga kokarin jawo jarin ketare na kasar Sin, amma annobar ba za ta iya canja yanayin jawo jarin waje da kasar Sin ke ciki a bana ba.

Rahoton UNCTAD ya nuna cewa, tabbas ne annobar COVID-19 da ta barke a farkon shekarar bana za ta kawo illa sosai ga kokarin da ake yi na zuba jari kai tsaye a wasu kasashen duniya, mai iyuwa ne yawan irin wannan jarin zai raguwar da ba a taba gani ba tun bayan barkewar rikicin hada-hadar kudi na duniya a shekarar 2008. Mr. Zhan Xiaoning, babban direktan sashen kula da zuba jari da masana'antu na hukumar UNCTAD yana mai cewa, "Wani kiyasin wucin gadi da aka yi kwanakin baya, ya nuna cewa, mai yiyuwa yawan jarin waje da za a zuba kai tsaye zai ragu daga kashi 5 cikin dari zuwa kashi 15 cikin dari. Idan za a yi nasarar kawo karshen yaduwar annobar a karshen watanni shida na bana, mai yiyuwa ne zai ragu da kashi 5 cikin dari. Amma idan annobar za ta ci gaba da bazuwa har zuwa karshen shekarar bana, hakika, adadin zai kai kashi 15 cikin dari."

Wani binciken da hukumar UNCTAD ta gudanar kan kamfanoni mafi girma guda 100 wadanda suke kasuwanci a duk duniya, ya nuna cewa, kashi 2 daga cikin 3 na wadannan manyan kamfanoni 100, sun fitar da sanarwar cewa, annobar COVID-19 ta kawo musu illa. 41 daga cikinsu ribar da za su samu a bana za ta ragu, sakamakon haka, tabbas hakan zai kawo illa ga yadda za su yi amfani da ribar tasu wajen zuba jari a ketare. Bugu da kari, kimanin rabi daga cikin kamfanoni dubu 5 mafiya girma a duk duniya, sun yi ha sashen cewa, yawan ribar da za su iya samu a bana zai ragu da kimanin kashi 9 cikin dari. Sannan annobar za ta kawo illa sosai ga galibin manyan kamfanoni na kasashe masu samun saurin ci gaban tattalin arziki. Yawan ribar da za su iya samu zai ragu da kimanin kashi 16 cikin dari.

A waje daya, Mr. Zhan Xiaoning ya bayyana cewa, ko da yake annobar za ta kuma kawo illa ga kasar Sin sakamakon sauyin yanayin zuba jarin da duk duniya ke ciki, amma ba za ta canja asalin yanayin jawo jarin waje da kasar Sin ke ciki ba. Mr. Zhan Xiaoning ya bayyana cewa, "Kasar Sin tana da nagartattun ayyukan yau da kullum. Sakamakon haka, asalin yanayin jawo jarin waje da kasar Sin ke ciki bai canja ba. Ingantattun abubuwan da ke akwai a kasar Sin ba su canja ba, sakamakon haka, babu abin da ya shafi karfin jawo jarin waje na kasar."

Zhan Xiaoning ya nuna cewa, abubuwa uku ne suke yi tasiri ga aikin zuba jari kai tsaye a ketare, wato manufa, da muhimman ayyukan yau da kullum dake da nasaba da tattalin arziki da kuma yanayin zuba jari maras sarkakiya. Bisa manufar da kasar Sin za ta dauka, tabbas ne za ta kara bude kofarta ga sauran kasashen duniya. Mr. Zhan Xiaoning ya kara da cewa, "Kasar Sin tana kara bude kofarta ga sauran sassan duniya, tana kuma kara daukar wasu sabbin matakai, kamar kirkiro tsarin yin amfani da jarin waje, hanyoyin jawo jarin waje, wato manufofin da kasar Sin take dauka sun fi jawo hankulan baki 'yan kasuwa idan aka kwatanta da kwatankwacin manufofin da sauran kasashen duniya, musamman wasu kasashe masu arziki wadanda suke kuma kokarin jawo jarin waje suke dauka. Alal misali, yanzu wasu kasashe masu arziki suna aiwatar da manufofin kare cinikayya, amma kasar Sin ta kara bude kofarta ga sauran sassan duniya maimakon daukar irin wadannan manufofin kare cinikayya."

Mr. Zhan Xiaoning ya kara da cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da girma, ko karuwarsa ta yi kadan ko ta yi sauri, tabbas ne tattalin arzikin kasar Sin na samun karuwa, yawan kudin shiga na kowane Basine ma na karuwa. Ana iya gano wannan yanayin da kasar Sin ke ciki. Sannan kuma, yanayin zuba jari da kasar Sin ke ciki ma, za a iya ganin cewa, kasar Sin tana da ingantattun ayyukan yau da kullum, da nagartattun kwadago da baki 'yan kasuwa suke bukata. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China