Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A karon farko tun Junairun bana, adadin sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 ya sauka zuwa maki 2 a kasar Sin
2020-03-07 16:26:31        cri
Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta bayyana a yau Asabar cewa, karon farko tun bayan ranar 20 ga watan Junairun bana, adadin sabbin masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 ya sauka zuwa maki 2 a kasar a jiya Juma'a.

Rahoton hukumar ya ce, ya zuwa jiya Juma'a, mutane 99 ne sabbin wadanda suka kamu da cutar, yayin da mutane 28 suka mutu a sakamakon cutar, a babban yankin kasar. Kuma an samu dukkan adadin wadanda suka mutu ne a lardin Hubei dake tsakiyar kasar.

Ta kara da cewa, daga cikin sabbin wadanda suka kamun, har da 24 da suka shigo kasar da cutar daga ketare. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China