Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wai sun gano akwai matsala kan matakin kasar Sin na yaki da COVID-19
2020-03-06 20:49:17        cri
Rahotanni kamar " Yadda kasar Sin take tace bayanai game da kwayar cutar da yadda ake yada farfagandar siyasa sun haifar da rudani" da aka wallafa a mujallar Wall Street Journal da "Cutar COVID-19 ta kassara karfin farfagandar kasar Sin" sun nuna cewa, kasar Sin ba ta samun nasara a yakin da take yi da annobar, don haka, akwai wata matsala a bangaren tsarin shugabanci da ma rahotannin da kafofin watsa labaran kasar ke watsawa.

Koda ya ke, baki dayan lamarin ya sha bamban.

Alkaluma na nuna cewa, tun daga tsakiyar watan Fabrairu, masu kamuwa da cutar na raguwa, yawan wadanda ke warkewa daga cutar na karuwa, Galibin lardunan dake wajen Hubei, da yawancin birane dake wajen Wuhan, sun ba da rahoton mutane kalilan ko ma babu wadanda suka kamu da ma mutu sanadiyar cutar a sanarwar da suke fitarwa a kowace rana. Haka kuma babu tashin hankalin al'umma, Harkokin rayuwa na gudana kamar yadda aka saba.

Tsarin Shugabanci? Yanzu haka, yawan gadajen kwantar da marasa lafiya sun dara marasa lafiya. Har ma an rufe wani asibitin wucin gadi, saboda karancin marasa lafiya. Haka kuma larduna da birane da dama na kasar Sin, sun rage matakansu na gargadin gaggawa. Harkokin kasuwanci suna dawowa sannu a hankali. Bugu da kari, an karawa jami'an da suka taka rawa girma, kana an maye gurbin wadanda ba su taka wata rawa ba da wasu.

Kafofin watsa labarai? Suna kokarin karfafa gwiwar al'umma, suna fadawa jarumai dake aiki a asibitoci da cikin al'umma, a hannu guda kuma, ana bankado matsaloli daban-daban tare da gano dalilan da suka haddasa su.

Dr. Bruce Aylward, jagoran tawagar WHO da ta ziyarci Wuhan da wasu biranen kasar Sin, ya shaidawa Vox.com abubuwa biyu da ya gani yayin da ya ziyarci kasar Sin

Na farko shi ne hanzari, " Ina ganin abu mai muhimmanci da za a koya daga kasar Sin, shi ne hanzari. Saurin gano wadanda suka kamu da cutar, da killace su, da wadanda suka yi mu'amala da su, hakan zai sa a samu gagarumar nasara.

Abu na biyu,. "Idan ka nutsu, ka daura damara, tare da fara gano wadanda suka kamu da wadanda suka yi ma'amala, hakika, lamarin zai canja yanayin barkewar cutar, da karya lagonta, tare da hana mutane da dama kamuwa har ma wadanda ke matsanancin hali za su rayu.

Suka daga al'umma ba sabon abu ba ne, musamman lokacin da aka samu barkewar wata annoba. Amma idan munanan labarai kalilan ne wadanda ba za su iya bayyana ainihin halin da ake ciki ba, shin ya dace a mai da hankali a kan watsa su? Wannan tamkar wata tatsuniya ce game da makafi da wata Giwa. Inda wasu mutane shida, suke ta musu game da yadda dabbar ta ke, saboda kowannensu ya taba wani bangare na jikin Giwar, kuma suke tunanin sun taba jikinta.

Amma wadannan rahotanni biyu sun sha bamban, wannan babban kuskure ne, sun shafawa kasar Sin kashin kaza ta hanyar ruruta abin da ba haka ya ke ba, da mayar da ra'ayi a matsayin gaskiya. Shin abin da suke fada gaskiya ne? Wasu gaskiya ne, amma an jirkita su da gangan.

Shin lamarin yana kara tabarbarewa ne? Morgan Stanley dai ya ayyana kasashen Sin da Singapore da Australia a matsayin wadanda za su kare hannayen jarinsu, yayin da ake fama da wannan annoba.(Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China