Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Labarin Shugaba Xi Jinping da masu yada ruhin mai aikin sa kai Lei Feng
2020-03-05 15:05:21        cri

Yau ranar 5 ga watan Maris, wata rana ce ta musamman ga Sinawa, kasancewarta ranar tunawa da ruhin Lei Feng, wani mai matukar himmatu da aikin sa kai, wadda aka kafa a shekaru 60 na karnin da ya gabata.

A wannan sabon zamanin da muke ciki yanzu ma dai, an ba ta wani suna na daban, wato ranar samar da hidimar aikin sa kai ta matasa. Ko da yake an canja sunan ranar, amma ma'anarta ba ta canja ba, wato domin yada akidun ainihi na salon gurguzu.

Tun bayan taron zama na 18 na wakilan 'yan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da aka kira a shekara 2012, babban sakataren jam'iyyar Xi Jinping ya ba da umurnin yada ruhin Lei Feng, da ma bunkasa sha'anin aikin sa kai, inda yake fatan dimbin masu aikin sa kai, da kungiyoyin aikin sa kai za su iya yin iyakacin kokarinsu wajen raya sha'anin a sabon zamanin da ake ciki domin ci gaba da yada ruhin Lei Feng.

A cikin shirinmu na yau, za mu waiwayi labarin Shugaba Xi Jinping da masu yada ruhin Lei Feng.

A watan Fabrairun shekarar 2014, kungiyar aikin sa kai ta Guo Mingyi, wadda ta zama abin koyi a fannin yin aiki tukuru, kuma Guo Mingyi ke jagoranta, ta rubuta wa Shugaba Xi Jinping wasika, domin gaya masa yadda suke ba da gudummawarsu wajen gudanar da ayyukan sa kai bisa ruhin Lei Feng. Ba da dadewa ba kuma, kungiyar ta samu wasikar da Shugaba Xi ya mayar mata a ranar 3 ga watan Maris na wancan shekarar, inda Xi ya bayyana cewa, ya kamata kowa ya koyi ruhin Lei Feng, haka kuma ya kamata a yi aikin sa kai a ko ina. Yayin da ake bukatar yawan hannu, ya dace a samar da tallafi, ta haka ne zaman al'ummarsu zai samu kyautatu. Haka kuma, Xi yana fatan masu aikin sa kai, za su iya yin iyakacin kokarinsu wajen ba da gudummawa, domin cimma burin farfadowar al'ummar Sin. Wasikar ta karfafa gwiwar Guo Mingyi da kungiyarsa. Guo yana mai cewa,

"Babban Darakta Xi Jinping ya gaya mana cewa, ruhin Lei Feng ba za a manta da shi ba har abada. Ya kamata kowa ya yi koyi da ruhin Lei Feng, haka kuma ya kamata a yi aikin sa kai a ko ina. Sa'an nan mu mai da kanmu a matsayin kusoshi, domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata."

Bayan da kasar Sin ta mai da hankali kan raya sha'anin aikin sa kai a wadannan shekaru, kuma dimbin mutane sun shiga sha'anin. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ana iya samun kungiyoyin masu aikin sa kai kamar kungiyar aikin sa kai ta Guo Mingyi fiye da su dubu 580 a duk fadin kasar, kuma yawan masu aikin sa kai da suka yi rajista ma ya zarce miliyan 110. Yanzu kuwa aikin sa kai na kyautata zaman rayuwar al'ummar Sin.

A watan Janairun shekarar 2019, Shugaba Xi Jinping ya yi rangadin aiki a unguwar Chaoyangli da ke birnin Tianjin, wadda ta kasance asalin kungiyar aikin sa kai ta unguwa a duk fadin kasar Sin. Bayan da ya fahimci yadda ake raya aikin sa kai a unguwar a shekaru fiye da 30 da suka gabata, Xi ya jinjinawa masu aikin sa kai cewa, aikinsu zai shiga tarihi. Ya ce,

"Masu aikin sa kai wani muhimmin bangare ne na sha'anin gudanarwa na zamanin yanzu, kyakkyawar halayya da aka samu sannu a hankali, sakamakon aikin sa kai abu ne mafi muhimmanci a cikin akidun ainihi na salon gurguzu. Kuma masu aikin sa kai jagorori ne a cikin wannan gudummawar, don haka ina jinjina muku."

A fagen daga na yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da ake gwagwarmaya a kai a wurare daban daban na Sin, ana iya ganin masu aikin sa kai a ko ina. Wasu na taimakawa likitoci wajen ceton masu fama da cutar, wasu na rarrabawa, da gudanar da aikin kayayyakin ceto, wasu na kokarin dakile yaduwar cutar a unguwannin al'umma, da ma tabbatar da zamansu yadda ya kamata.

Masu aikin sa kai za su fito a duk inda ake bukata. Zheng Xinyi, wata daliba dake gudanar da aikin sa kai a birnin Wuhan, ta kuma furta cewa,

"Hakika dai, a farkon bullar annobar, ina jin tsoronta, na damu da iyali da abokan karatu na da ma abokai na. Amma bayan hankali na ya kwanta, na fara tunani kan me zan iya yi ga zaman al'ummarmu da wannan birnin da muke kaunar sa sosai. Yanzu muna aikinmu ne a duk inda ake bukatar mu, muna kokarin daukar nauyi mai yawa a wuyanmu." (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China