Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yayin da ake tsaka da yaki da cutar COVID-19 sashen wasannin kasar Sin na nazari kan hanyoyin samun damammaki
2020-03-10 13:54:18        cri

Bayan bullar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin, an dage manyan gasannin kwallon kafa na kasar, kamar CBA, da super league da ma sauran manyan gasannin da kulaflika ke bugawa. Kaza lika manyan gasanni na kwallon kafar mata da wasannin neman gurbin shiga gasar damben boxing na Olympic, wadanda a baya aka tsara gudanarwa a nan kasar Sin, a yanzu an mayar da su wasu kasashen na daban. Har ila yau, an dage gasar wasannin hunturu na kasar Sin karo na 14, da ma gwajin farko na gasar Olympics na lokacin hunturu na Beijing. Bugu da kari an soke gasar kasa da kasa na wasan kankara ajin kwararru na kasa da kasa na "alpine" wanda aka tsara gudanarwa a tashar yanqing.

Baya ga fannin gasanni, barkewar wannan cuta ya kuma shafi dukkanin sassan da suka jibanci wasanni. Hakan dai ya zamewa masu ruwa da tsaki a harkar wani kalubale mai tsanani.

Babbar raguwar hada hada a harkokin wasanni

Daraktan sashen nazarin tattalin arziki mai nasaba da wasanni, a cibiyar bincike dake jami'ar ilimin cinikayya da tattalin arziki na Sin Wang yuxiong, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, annobar COVID-19 ta yi babban tasiri ga harkar wasanni. Har ila yau, bullar cutar ya zo a gabar da ake bukukuwan sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta Sin, wanda lokaci ne da harkokin wasanni masu nasaba da 'yan yawon bude ido ke kaiwa matsayi na koli. Baya ga wannan, da yawa daga kamfanonin dake fitar da kayayyakin wasa zuwa kasashen waje, ba za su iya fara sarrafa hajojin su ba bisa tsarin aikin su na yau da kullum, wanda hakan ke haifar da karyewar kwangiloli, ko watsi da odar masu sayayya, lamarin da ya haifar da babbar asara.

Wang yuxiong, ya ce "Abu mafi daga hankali shi ne, duba da cewa masana'antar harkokin wasannin kasar yanzu ne take tasowa, tana kunshe da kananan masu sana'oi da dama, wadanda kudaden su na gudanar da hada hada ba su da yawa, wasu kuma suna da rauni na kasuwanci." Ga irin wadannan kamfanoni, tasirin bullar wannan cuta ya wuce na karancin kudin shiya, batu ne ake yi na dorewar su ko kuma karayar su baki daya."

Daya daga wuraren wasannin kankara da aka rufe sakamakon bullar wannan annoba shi ne wurin zamiyar kankara na Altay. Daraktan kula da wurin shizhiqiang ya bayyana damuwa game da hakan yana mai cewa, "wannan ne lokacin samun kudi. Rufe wajen ya bijiro da batun biyan albashin ma'aikata, da batun kayan aiki da dama da muka sayo gabanin shigowar lokacin hunturu, don haka akwai babban matsi, game da kudaden da muka kashe ba tare da samun riba ba."

A daya bangaren kuma, an dage, ko an soke wasanni da jiragen ruwa ko "sailing" a turance, ciki hadda tsaren jiragen ruwa da ke gudana a Huizhou, da gasar kasa ta tseren kwale kwale ta shekara shekara. Kungiyoyi da masu wasan da kuma kamfanoni masu ruwa da tsaki sun fuskanci kalubale sakamakon hakan. A cewar shugaban cibiyar wasannin ruwa ta "Tian haifeng" dake birnin Tianjin Zhai qilu, an dage wasannin kankara da na dusar kankara kala kala, da aka shirya gudanarwa a wurare daban daban.

Laluben damammaki a lokutan wahalhalu

Yanzu haka dai babu abun da ya rage ga fannin wasannin kasar Sin a irin wannan gaba da ake fuskantar tasirin cutar COVID-19, illa kokarin kaucewa karaya, kana daga bisani a yi kokarin samun ci gaba.

A cewar Wang yuxiong, ya dace a rungumi bunkasa samun horo, da amfani da wasu na'urorin wasanni masu dauke da fasahohin zamani, da gina fannin ilimi, da atisayen wasanni ta yadda za a iya samar da horo ga masu ruwa da tsaki ta yanar gizo. Sai kuma batun fadada hada hadar kasuwanci ta fanni ta yanar gizo.

Shi kuwa wanda ya kirkiri cibiyar kwallon Kwando ta Youken Ding renhai cewa ya yi, tuni cibiyar sa ta mayar da mafi yawa na ayyukan ta zuwa yanar gizo, domin cin gajiyar dalibai da matasa.

Wasu sassan masu ruwa da tsaki da ke bakin aiki a wannan gaba, na daukar matakai mabanbanta domin tabbatar da ci gaban sana'ar su; ga misali; babban manajan kamfanin kwale kwale na Wanhang Lixiaohuan, da daraktan kwamitin dake lura da harkokin matasa, sun dauki wasu matakai guda 4. Inda aka tsara masu horas da 'yan wasa za su rika aiki sau 3 a ko wane mako, sa'an nan a rage albashin su zuwa rabi. Sai bangaren ma'aikatan gudanarwa da za su rika yin cikakken aiki, amma za a rage albashin su zuwa kaso 70 bisa dari. Sai tawagar masu samun horo, inda za a samarwa masu ba da horo da litattafai, da kayan aiki game da sadarwa, da jagoranci, da na sanin makamar aiki a ko wane mako. Mataki na uku shi ne tsara ayyuka, ta yadda za su dace da yanayin da ake ciki bayan bullar wannan annoba; Na hudu kuma karkata akalar abokan hulda, ta yadda za su amince da yin hulda ta yanar gizo, tun daga kwasa-kwasai na farko har zuwa ajin kwararru, kana a yi bayani dalla dalla game da yanayin gudanar da wasanni, da ka'idoji, da dabarun kwarewa, da gwajin wasanni da gasanni ta wannan hanya.

Shi zhiqiang daya ne daga masu aikin yayatawa, da tallata wannan harka. Ya kuma yi imanin cewa, asara ta riga ta shafi wannan fanni, don haka zai zage damtse wajen tallata wasannin lokacin hunturu da za su gudana a shekara mai zuwa, da ma wasannin da za a iya gudanar da su a lokacin bazara, ciki hadda gina wurin wasan zamiya na kankara da ake samarwa daga injuna, da wasannin kalankuwar kade kade da raye raye, da kasuwannin dare, da wasan hawa tsaunuka da babur, da na hawa balo, da dai sauran su. Zhaiqilu, wanda ofishin sa ke kula da wasu harkoki a ketare, yanzu haka na shirin mayar da wasu ayyuka zuwa yankin Chiang mai, na kasar Thailand.

A wani bangaren kuma, bukatar yin wasannin motsa jiki a gida, ta sanya kasuwar masu samar da horo a fannin fara bunkasa. Kwararrun 'yan wasa irin su huang xiaoming, sun samar da dandali ta bidiyo domin ba da horo, kana 'yan wasa da suka taba lashe lambobin yabo a gasar Olympics irin su gao min da xulijia, su ma sun dora bidiyon wasannin motsa jiki ta bidiyo a kafar yanar gizo. Hakan yana da matukar muhimmanci, kasancewar motsa jiki a gida na karawa jikin dan adam karfin tunkarar cututtuka, ciki hadda wannan annoba da ake yaki da ita. Da tallafin hanyoyin sadarwa na yanar gizo irin su douyin da kuaishou, ana iya yin kwasa kwasai daga gida, a kuma samu fa'idar motsa jiki yadda ya kamata.

Takarar samar da wuraren motsa jiki a yanar gizo

Alkaluman kididdiga da cibiyar lura da harkokin wasanni ta kasa da kasa ta yanar gizo ko PP ta fitar, sun nuna matsakaicin yawan mutane dake halartar wasannin lokacin bikin bazara ya karu zuwa kaso 151.4 bisa dari, idan an kwatanta da na lokacin bikin bazara na bara. PP ma ta kaddamar da shirin talabijin na wasannin motsa jiki a lokacin da wannan cuta ta barke, domin taimakawa masu sha'awar yin wasannin ci gaba da yin hakan a gida, wanda hakan zai karfafa gwiwar mutane wajen ci gaba da motsa jikin.

Mene ne makomar wasanni bayan wannan cuta?

Yayin da masu ruwa da tsaki ke ci gaba da bayyana damuwa game da yaduwar cutar, da batun yiwuwar farfadowar masana'atun harkokin wasanni, ana ci gaba da hasashen yanayin da wadannan masana'antun za su tsinci kan su ciki.

Fu danqing dake aiki a fannin wasannin kwale kwale ya bayyana damuwa kan hakan, duk da a cewar da zarar an kawo karshen wannan annoba harkokin wasanni za su samu farfadowa. Ya ce "Muna gaggauta tsarin samar da horo da cibiyoyi masu inganci, za mu yi amfani da sauran lokutan domin kyautata fannin ba da horo. Bayan barkewar wannan annoba, za mu ci gaba da amfani da dandali, da albarkatu, wajen taimakawa kungiyoyi da rukunonin masu wasanni wajen rage kudaden gudanar da gasanni da samar da horo, a lokaci guda kuma, muna son kara yayata ayyuka na inganta hada hadar cinikayya da rage radadin annobar ga fannin wasanni."

Fu danqing ya kara da cewa "Gagarumin sauyi da ci gaba da aka samu a fannin wasannin kasar a baya bayan nan, ya biyo bayan kyakkyawan ginshikin tattalin arziki da ci gaban zamantakewa da aka samu a kasar Sin, wanda bullar wannan cuta ba zai rushe ci gaban da aka samu ba". Ya ce daga karshe dai, bayan wannan annoba, bunkasar fannin wasanni zai ci gaba da samun tagomashi, kuma fannin tsara manufofi zai ci gama da samun ci gaba, wanda hakan zai taimaki fannin wasannin baki daya. Don haka daga karshe dai, makomar fannin wasanni na da haske, ba kuma zai gurgunce gaba daya ba."

"To sai dai kuma muna fatan gajeran tasirin da fannin wasannin zai fuskanta ya zama takaitacce sosai, wanda kuma hakan na bukatar samar da kudade. Muna fatan ganin hakan ta hanyar hadin gwiwa tsakanin dukkanin sassa, kaso mai yawa na kanana, da matsakaita da manyan kamfanoni za su ci gaba da rayuwa. Muna da yakinin cewa, bayan wannan annoba, sashen wasanni na Sin zai samu makoma mai haske.

(Amina,Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China