Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Waklin kasar Sin ya bayyana ci gaban da kasar ta samu a fannin yaki da cutar COVID-19
2020-03-03 21:07:06        cri
Wakilin din din din na kasar Sin a MDD kana shugaban kwamitin tsaron majalisar na watan Maris Zhang Jun ya bayyana irin nasarorin da kasarsa ta samu a yaki da cutar numfashi ta COVID-19 gami da kokarin da ta ke na cimma nasarar manufofinta na raya kasa a wannan shekara.

Jami'in wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai game da aikin kwamitin, ya ce, domin ganin bayan wannan cuta, an dauki managartan matakai masu karfi na hana yaduwa, kuma duniya ta kalli yadda gwamnati kasar Sin ta dauki matakan da suka dace, da karfin hadin kan al'ummar kasar da karfin tsarin kasar.

Da yake bayani game da nasarar da kasar ta ke fatan cimmawa a fannin raya kasa, biyo bayan bullar annobar COVID-19, Zhang, ya ce, a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin tana sane da nauyin dake bisa wuyanta, kuma tana daukar jerin managartan matakai, ciki har da manufofi na tallafi da ta dauka ta fannonin harkokin kudi, da haraji, da masana'antu, don ganin ma'aikata sun dawo bakin aiki da samar da yanayin da ya dace na ganin kamfanoni sun dawo aiki kamar yadda ya kamata, ta yadda za a bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ya kara da cewa, kasar Sin za ta rage tasirin bullar cutar da yin aiki tukuru, don cimma nasarar manufar da ta sanya a gaba a fannin tattalin arziki da jin dadin jama'a.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China