Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba ta taba fuskantar rikicin addini ba
2020-03-03 13:26:08        cri

Kwamitin kare hakkin Bil Adama na MDD yana gudanar da taronsa karo na 43 a birnin Geneva, inda a jiya Talata an yi muhawara da wakilan musamman kan 'yancin bin addini, inda wakiliyar musamman ta kasar Sin kan batun kare hakkin Bil Adama Liu Hua ta nuna cewa, addinai daban-daban na zama tare cikin jituwa a kasar Sin, kuma ba a taba rikicin addini ba har zuwa yanzu.

Liu Hua ta ce, bisa tanade-tanaden tsarin mulkin kasar Sin, wata hukuma ko kungiyoyi ko daidaikun mutane, ba su da ikon tilastawa mutane bi ko magance bin wani addini, sannan kuma an haramta nuna bambanci kan mutanen da suke bin wani addini, ko kuma wadanda ba su bin addini. Ya ce a kasar Sin ana samun masu bin addinin Budda da Taoism da kuma Musulunci da Katolika da sauransu, sannan kuma a kasar akwai kungiyoyin addinai fiye da 5500, har da  kwalejojin addinai kimanin dari, da wurare ibada sama da dubu 140. Har ila yau, Sin na da wuraren ibada na mata mabiya musulunci fiye da dari. Tana mai cewa, wannan ya nuna cewa, addinai daban-daban na zama tare cikin jituwa a kasar Sin, ba tare da rikici ba. Matakin kuma ya bayyana al'adun kasar Sin na yin hakuri da juna tsakanin bangarori daban-daban, da kuma bayyana cewa, manufofin da gwamnatin Sin ke dauka kan addinai sun dace da yanayin da kasar ke ciki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China