Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na kokarin hana shigowar cutar COVID-19 daga ketare a yayin da take dakile cutar a gida
2020-03-02 12:40:56        cri

A yayin taron manema labaru da kwamitin rigakafi da dakile cutar numfashi ta COVID-19 cikin hadin gwiwa na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya jiya Lahadi, an ce, yanzu kasar Sin na daukar matakai bisa doka domin hana shigowar cutar daga ketare a yayin da take kokarin dakile cutar a gida, ta yadda za ta iya bayar da gudummawarta wajen tabbatar da tsaron lafiyar al'ummomin shiyya-shiyya, har ma da na duk duniya.

A 'yan kwanakin baya, yanayin fama da cutar numfashi ta COVID-19 da sauran kasashen duniya ke fuskanta ya kara tsanani sosai, sakamakon haka, kasar Sin na fuskantar hadarin shigowar cutar daga ketare. Mr. Lin Wei, babban direktan sashen kiwon lafiya da kebe marasa lafiya na babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu ana daukar matakai bisa ilmin kimiyya a dukkan tasoshin kwastam wajen hana fitar da cutar zuwa ketare, tare da hana shigowarta kasar Sin daga ketare. Mr. Lin yana mai cewa, "A lokacin da yanayin fama da cutar yake samun sauye-sauye a lokuta daban daban, mun gayyaci masana wadanda suka fito daga hukumomi daban daban, kuma kwararru kan ilimi daban daban, da suka yi aiki wajen nazartar halin da ake ciki, kuma suka fitar da ra'ayoyinsu game da matakan dakile cutar da ya kamata a dauka a tasoshin kwastam. Bisa ra'ayoyinsu ne, muka dauki matakai daban daban domin kokarin hana shige da ficen cutar."

Bugu da kari, hukumar kula da masu kaura ta kasar Sin ta kuma dauki matakai daban daban na hana shigowar cutar kasar Sin daga ketare. Mr. Liu Haitao, babban direktan sashen binciken masu kaura a bakin iyakar kasar Sin ya bayyana cewa, "Kafin isowar kowane jirgin saman fasinja kasar Sin daga ketare, bisa bayanan kwamfuta da ta samu, hukumar kula da masu kaura ta kasar Sin ta fara nazarin dukkan fasinjojin da suka fito daga kasashe da yankuna masu fama da cutar. A waje daya, ta sanar da bayanan wadanda suke dauke da cutar ga kananan hukumomi. Sannan za mu dauki matakan hadin gwiwar hukumomin kasashe da yankuna wadanda suke tinkarar cutar, wajen musayar bayanan masu dauke da cutar, wadanda mai yiyuwa za su yi tafiya tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a iya yin kokarin hana yaduwar cutar tsakanin kasa da kasa."

Yanzu, cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa a wasu kasashe da yankuna a duniyar. Bisa wannan halin da ake ciki, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman fasinja ta kasar Sin ta dauki matakai daban daban bisa yanayi daban daban da kowace kasa ko kowane yanki ke ciki. Mr. Zhu Tao, babban direktan sashen tsara ka'idojin zirga-zirgar jiragen saman fasinja na kasar Sin yana mai cewa, "Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman fasinja ta kasar Sin ta dauki jerin matakan hana yaduwar cutar ta jiragen sama, alal misali, a kullum ana fesa maganin kashe kwayoyin cutar a jiragen sama da filayen sauka da tashin jiragen, tare da kuma auna zafin jikin fasinjoji. Bugu da kari, muna amfani da dabaru da fasahohin da muke da su wajen tinkarar cutar da takwarorinmu na sauran kasashen duniya. Yanzu, muna tattaunawa da wasu kasashe wajen kafa ma'auni iri daya na tinkarar cutar domin hana yaduwarta tsakanin kasa da kasa ta jiragen sama. Tabbas hukumarmu za ta kara hadin gwiwa da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman fasinja ta kasa da kasa wajen kyautata ma'aunan tinkarar cutar da ya kamata kowane kamfanin zirga-zirgar jiragen saman fasinja na duk duniya ya bi wajen tinkarar hadarin kiwon lafiya cikin hadin gwiwa bisa ma'auni daya."

Cutar numfashi ta COVID-19 yanzu ta kasance wani kalubale da duk duniya ke fuskanta, sakamakon haka, ana bukatar al'ummomin kasa da kasa su yaketa cikin hadin gwiwa. Mr. Cui Aimin, babban direktan sashen kula da harkokin jama'a a ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, bayan bullowar cutar, gwamnatin kasar Sin ta dauki kwararan matakan tinkarar cutar daga dukkan fannoni, ta kuma bayar da gudummawarta sosai wajen hana yaduwar cutar tsakanin kasa da kasa. Mr. Cui yana mai cewa, "Yanzu, annobar na yaduwa a wasu kasashen duniya. Tabbas za mu kula da yadda annobar take yaduwa a wasu kasashe. Muna fatan za mu iya hada kan sauran kasashen duniya wajen hanawa da kuma tinkarar annobar, ta yadda za mu iya tabbatar da lafiya da tsaron al'ummomin duniya baki daya tare." (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China