Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Najeriya: Cutar numfashi ta COVID-19 ba za ta yi tasiri sosai ba ga hadin kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Najeriya ba
2020-02-24 14:14:30        cri

 

Kasar Najeriya, ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, tasirin da cutar ke haifarwa tattalin arzikin kasar na jawo hankalin al'ummar kasar. Wasu masanan kasar ta Najeriya suna ganin cewa, cutar COVID-19 ba za ta yi tasiri sosai ga tattalin arzikin kasar da ma hadin kan dake tsakaninta da kasar Najeriya a fannonin tattalin arziki da cinikayya ba.

 

 

Alkaluman kididdigar da hukumar kwastan ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a shekarar 2019, darajar cinikayya a tsakanin kasashen Sin da Najeriya ta kai dalar Amurka biliyan 19.27, wato ta karu da kashi 26.3 cikin dari bisa na makamancin lokacin shekarar 2018. Ikenna Emewu, daraktan cibiyar kafofin watsa labaru na Afirka da Sin ta kasar Najeriya, wanda ya dade yana mai da hankali kan harkokin hadin kan kasashen biyu a fannoni daban daban, yana ganin cewa,

"Gaskiya bullar cutar numfashi ta COVID-19 ta kawo cikas ga tattalin arzikin kasar Sin, kuma babu wata kasa da za ta iya kaucewa daga cutar, za kuma ta haddasa tafiyar hawainiya ga tattalin arziki, amma ba zai yi tasiri mai tsanani kamar yadda aka yi tsamani ba."

 

A nasa bangaren, daraktan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta kasar Najeriya Charles Onunaiju yana ganin cewa, ko da yake kasar Sin na fuskantar kalubale sakamakon cutar numfashin, amma tattalin arzikin kasar na cike da karfi sosai, duk da haka, ana iya bayyana wani gagarumin hasashe kan makomar tattalin arzikin kasar. Ya ce,

"Ina tsammani tasirin cutar, ba zai durkusar da tattalin arzikin kasar Sin ba. Na san cewa, tattalin arzikin kasar Sin na cike da karfi wajen tinkarar kalubale. Na yi imanin cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana iya ci gaba da samun bunkasuwa kamar yadda aka tsara."

Najeriya kasa ce da kasar Sin ta fi samun kwangilar ayyuka a Afirka, kuma kasuwa mafi girma ce da kasar Sin ke shigar da kayayyakinta a nahiyar, kana ita ce babbar abokiyar cinikayya ta uku ta kasar Sin, baya ga zama muhimmiyar kasar da Sin ke zuba jari a nahiyar Afirka. Ikenna Emewu, daraktan cibiyar kafofin watsa labaru na Afirka da Sin ta kasar Najeriya ya bayyana cewa, bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka, tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka da Sin da Najeriya za su ci gaba da raya karfinsu. Ya ce,

"A gani na, ba za a kawo cikas ga hadin kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen Sin da Najeriya, da Sin da Afirka ba, saboda ana gudanar da hadin kan ne bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin kasar Sin da Afirka. Ban ga alamar tattalin arzikinsu zai durkushe sosai ba, kuma ban ga wane irin mummunan tasiri za a iya yi wa hadin kan tattalin arziki a tsakanin Sin da Afirka ba."

 

Masani a fannin harkokin kasar Sin na jami'ar Abuja ta kasar Najeriya, Dr.Ibrahim Sheriff ya bayyana cewa,

"A gani na, gwamnatin kasar Sin da jama'arta suna da kwarewa wajen jure yanayin da suke ciki, kuma suna da karfi sosai wajen shawo kan annobar. Na yi imanin cewa, nan da ba dadewa ba, za a kawo karshen cutar, wadda za ta kasance tarihi. Don haka, in an yi hangen nesa, ina tsamani annobar ba za ta hana ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ba, bayan an kawar da ita, tattalin arzikin kasar ta Sin zai kara wadata." (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China