Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana kokarin farfado da aikin masana'antu a kasar Sin
2020-02-21 13:07:06        cri

A 'yan kwanakin baya, gwamnatocin wurare daban daban na kasar Sin, sun fitar da dimbin matakan hanzarta farfado da aikin masana'antu wadanda aka yi musu illoli sakamakon barkewar cutar numfashi ta COVID-19. Wasu kamfanoni wadanda suke kokarin gina wasu muhimman manyan ayyukan yau da kullum suna kokarin komawa bakin aiki, a lokacin da suke kokarin yakar cutar.

Alal misali, gwamnatin garin Yiwu, wato cibiyar cinikin kananan kayayyakin yau da kullum mafi girma a kasar Sin, ta ce akwai kyauta, ga dukkan kamfanoni masu zaman kansu, da wasu kamfanoni wadanda ba su yi rajista a garin ba, amma suka samu kwangilolin gina wasu muhimman ayyuka a garin. Kamar kudin alawus ga kamfanoni wadanda suka yi hayar ababen hawa, domin komowar 'yan kwadago daga sauran sassan kasar, da mayar da kudin tikiti ga 'yan kwadago wadanda suka hau jiragen kasa ko ma masu ababen hawa da suka koma bakin aiki na kamfanonin garin Yiwu. Kamfanin samar da kayan kare jikin 'yan wasannin motsa jiki na Steriger a lardin Zhejiang, ya ci gajiyar wannan manufa. A 'yan kwanakin baya, kamfanin ya yi hayar wasu manyan motoci domin dawowar sabbi da tsoffin ma'aikata 52 daga garin Ludian na lardin Yunnan. Nisa tsakanin garin Ludian da garinYiwu ya kai fiye da kilomita 2000. Mr. Hong Zhuangming, shugaban kamfanin ya bayyana cewa, "Sabo da mu yi hayar mota wajen dawowar ma'aikatanmu, mun farfado da aikin mu cikin sauri. Sabo da haka, yawan kudin da muka yi tsimi ya kai kudin Sin yuan dubu 60 sakamakon alawus daga gwamnatin garin Yiwu. Yanzu muna da imani wajen cimma burin mu na ninka yawan kayayyakin da za mu iya samarwa a bana."

Sannan kuma, ana kokarin farfado da aikin gina muhimman manyan ayyukan da ake yi yanzu. Kawo yanzu, yawan muhimman manyan ayyukan da aka riga aka farfadowa, da sake ginawa sun kai 264, a yayin da aka kaddamar da wasu sabbin muhimman manyan ayyuka 32 a yankin Guangdong da Hongkong da Macau. Mr. Chen Dewei, direktan sashen daidaita harkokin yau da kullum a hukumar ba da hidima bisa bayanan kwamfuta ta lardin Guangdong, yana mai cewa, "Dole ne a rage dukkan matakan da ya kamata a rage. Idan an gamu da matsaloli, ba damuwa, ya dace a gaya mana. Za a iya nazari bisa bayanan kwanfuta, sannan za a iya samar da wasu shirye-shiryen kawar da matsaloli ga kamfanoni domin biyan bukatun da suke da su. Dole ne hukumomin gwamnati su biya bukatun da kowane kamfani yake da su."

Aikin shimfida layin bututun iskar gas na gabas dake tsakanin kasashen Sin da Rasha na daya daga cikin layuka 4 na bututun iskar gas dake tsakanin kasashen biyu. A garin Beizhen na birnin Jingzhou a lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin, inda ake aikin shimfida layin bututun iskar gas na gabas dake tsakanin kasashen Sin da Rasha, bayan an auna yawan zafin ma'aikata 70, da kuma samar musu abubuwan rufe baki, sun koma bakin aikinsu, tare da injunan da suke sarrafawa. Mr. Cai Deyu, mataimakin direktan dake kula da aikin, ya bayyana cewa, "Yawan ma'aikata wadanda suka fito daga sassa daban daban na kasar Sin, kuma suke aikin shimfida batutun ya kai fiye da dubu 6. Ko da yake muna fuskantar matsalolin karancin kayayyakin aiki da ma'aikata, muna kokarin farfado da aikin mu bisa shirin da aka tsara, domin tabbatar da ganin mun samar da ingantaccen layin batutun iskar gas na gabas, da ke tsakanin kasashen Sin da Rasha, ta yadda za a iya tabbatar da layin ya fara aiki a karshen shekarar bana."

A birnin Shanghai, kungiyoyin nazari da kuma kera jirgin saman fasinja samfurin C-919, da ARJ21, da kuma C-929, sun hanzarta komawa bakin aikin su domin kokarin samun sabon ci gaba bisa shiri, wajen nazari da yin gwaje-gwaje, da kuma kera wadannan jiragen saman fasinja. Mr. Wu Xing, matukin sabon jirgin saman fasinja samfurin C-919 yana mai cewa, "Yanzu, an riga an fara gwada tashi da saukar dukkan jiragen sama samfurin C-919 guda 6. A lokacin da muke gwada ingancin su a wurare 4 na kasar Sin, muna kuma yin aikin tantance su a filin jiragen sama." (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China