Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda Sinawa suke jin dadin zama a gida a wannan lokaci na musamman
2020-02-17 16:08:42        cri

Sinawa su kan ziyarci 'yan uwa da abokansu, shirya bukukuwa iri daban daban, da kuma zuwa yawo a lokacin bikin bazara. Amma, saboda yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a lokacin bikin bazara na bana, dukkanin mutanen Sin ba su tafi waje ba, inda suke zaune a gidajensu domin hana yaduwar cutar tsakanin mutane. Ga kuma yadda wasu mutanen Sin suke jin dadin zamansu a gidaje.

Malama Zhang na birnin Xiangyang na lardin Hubei ta yi zane-zane sama da guda 10, da 'ya'yan tsiron "Sunflower" 807, bayan ta sa zane-zanen a shafinta na yanar gizo, ta samu "likes" sama da dubu 40.

Wani iyalin dake zaune a birnin Dalian na lardin Liaoning malamai na motsa jiki ne, sun sa bidiyo na yadda suke wasan Ping-Pong a gida a shafinsu na intanet, yawan mutanen da suka kalli bidiyon ya kai sau sama da dubu 6.

Sinawa suna zama a gidajensu, ba sa fita waje, domin ba da gudummawarsu wajen hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a tsakanin mutane.

Duk da suna cikin mawuyacin hali, amma ba su daina neman jin dadin zamansu ba, sabo da akwai ma'aikatan likitanci dake gudanar da aikin ceto. Akwai ma'aikata na unguwanni, da 'yan sanda da dai sauransu, dake ba da gudummawarsu wajen kiyaye zaman karko na zamantakewar al'umma.

Shi ya sa, a wannan lokaci na musamman, mutanen Sin suna iya kwantar da hankulansu, domin suna da imani kan kasarsu, kuma cutar ba za ta rushe wadanda suke son zaman rayuwarsu a duniya ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China