Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Dalilin Da Ya Sa Kasar Sin Ke Da Imanin Samun Nasara A Kokarin Dakile Annoba
2020-02-17 12:28:00        cri

 

Har zuwa ranar 16, a sauran wuraren kasar Sin ban da lardin Hubei, adadin sabbin wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 yana ta raguwa cikin kwanaki 13 a jere. Ban da haka, wasu fiye da dubu 10 sun riga sun warke daga cutar. Hakan na nufin matakan da kasar Sin ta dauka na dakile cutar sun yi amfani, kana an samu shawo kan yanayin bazuwar cutar.

A ranar 15 ga wata, Tedros Ghebreyesus, babban magatakardan hukumar lafiya ta duniya WHO, ya bayyana a wajen wani taron da ya shafi harkar tsaro da ya gudana a birnin Munich na kasar Jamus, cewa kasar Sin ta yi namijin kokari da sadaukarwa, don dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, saboda haka, kasar ta cancanci yabo daga gamayyar kasa da kasa. Jami'in na kira ne ga bangarorin kasa da kasa don su yi nazari kan hakikanin abun da ya faru, sa'an nan ya bukaci kafofin watsa labaru da su yi kokarin hana yaduwar jita-jita da karairayi.

Duk da haka, ba a rasa wasu mutanen da suke zargin kasar Sin da gaza daukar matakin da ya dace ba, inda har suka ce tattalin arzikin kasar Sin zai samu koma baya sosai. Dangane da zancen, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya shaidawa wakilin kamfanin Reuters a kwanakin baya cewa, kasar Sin tana da imani da cikakkiyar kwarewa wajen samun nasara a yakin da take yi da cutar COVID-19.

Dalilin da ya sa kasar Sin ke da imanin, shi ne domin shugabannin kasar sun nuna basira da kwarewa a fannin jagorantar ayyukan dakile cutar. A ranar farko ta bana bisa kalandar gargajiyar Sin, wadda ke da ma'anar musamman bisa al'adun kasar, shugaban kasar Xi Jinping ya kira wani taro, inda ya ba da umarni ga daukacin al'ummar kasar Sin su fara daukar matakan tinkarar annoba tare, lamarin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar. Daga bisani shugaban ya sa aka kafa wata tawagar shugabanni ta musamman don jagorantar ayyukan hana yaduwar cutar COVID-19.

Sa'an nan wani dalili na daban da ya ba Sinawa damar samun kwarin gwiwar tinkarar annobar shi ne, nagartaccen tsarin mulkin kasar. Tun bayan barkewar annobar, nan take gwamnatin kasar Sin ta gabatar da wani tsari na tara kayayyaki daga dukkan sassa daban daban na kasar, inda ake daukar matakai mafi karfi wajen tinkarar annobar. Cikin kankanin lokaci, an samu kafa wasu manyan asibitoci na musamman, sa'an nan likitoci na wurare daban daban da rundunar sojin kasar fiye da dubu 10 sun tafi birnin Wuhan, inda yanayin bazuwar cutar ta fi tsanani, don ba da taimako a can. Yayin da daukacin jama'ar kasar suke tsayawa a gida bisa umarnin gwamnati, don magance bazuwar cutar COVID-19. Wadannan kwararan matakai sun tabbatar da samun biyan bukata a kokarin dakile yaduwar cutar.

Ban da wannan kuma, wani abun da ya bai wa kasar Sin imani shi ne yadda gamayyar kasa da kasa ke kokarin taimaka mata. Samun labarin bullar cutar ke da wuya, nan take kasar Sin ta sanar da labarin ga hukumar WHO da kasashe daban daban, don a fara daukar matakan kandagarki a duk duniya. Wannan kokari ya sa ba a samu bazuwar cutar COVID-19 zuwa sauran kasashe sosai ba, inda yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasashen waje bai kai kashi 1 bisa kashi dari ba cikin dukkan mutanen da aka zaton sun kamu da cutar a duniya. Yadda kasar Sin ke kokarin daukar matakai masu amfani a bayyane, ba tare da rufa-rufa ba, ya sa kasar samun goyon baya sosai daga gamyyar kasa da kasa. Inda shugabannin kasashe da na kungiyoyin kasa da kasa fiye da 160 suka aike da sakwannin jaje da nuna goyon baya ga kasar Sin. Sa'an nan gwamnatoci da al'ummun kasashe fiye da 10 sun samar da dauki ga jama'ar kasar Sin.

Ban da haka, kasar Sin ta samu kwarin gwiwa kan samun nasarar dakile cutar ne, saboda ta fahimci kalubalen da take fuskanta, sa'an nan ta riga ta dauki wasu matakai don tinkarar sa. Ga misali, a fannin aikin tabbatar da lafiyar jama'a, kasar Sin za ta yi kokarin nazarin dukkan fasahohin da ta samu a yakin da take yi da annobar COVID-19 a wannan karo, don kara kyautata dabarunta na kare lafiyar jama'a. Ban da haka kuma, a fannin rage illar da cutar ta haifar ga tattalin arzikin kasar Sin, kasar za ta mai da kokarin tabbatar da jin dadin zaman rayuwar jama'a ya zama aiki na farko da za a dinga lura da shi. Sa'an nan za ta daidaita huldar dake tsakanin aikin hana yaduwar cuta, da farfado da ayyukan samar da kayayyaki. A karshe dai za a ga bayan annobar, yayin da kasar Sin za ta sake samun karuwar tattalin arzikinta cikin sauri. (Mai Fassarawa: Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China