Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabar IMF: Bai dace ba a tantance tasirin da annobar numfashi ke kawowa Sin a yanzu
2020-02-13 12:36:47        cri

Jiya Laraba 12 ga wata, agogon kasar Amurka, shugabar asusun ba da lamuni ta duniya Kristalina Georgieva ta karbi intabiyun da wakilin babban rukunin gidajen radiyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice ya yi mata a birnin Washington na kasar, inda ta bayyana cewa, yanzu haka gwamnatin kasar Sin tana daukar matakan da suka dace yayin da take kokarin shawo kan cutar numfashi, a don haka bai dace ba a tantance tasirin da annobar take kawowa tattalin arzikin kasar a halin da ake ciki yanzu.

Madam Georgieva ta gayawa wakilinmu cewa, abu mafi muhimmanci shine an lura cewar, al'ummumin yankunan dake fama da yaduwar annobar suna cikin mawuyancin hali mai tsanani, ya kamata a kara maida hankali kan aikin yakar annobar, ta kara da cewa, asusun bada lamunin duniya yana ganin cewa, gwamnatin kasar Sin tana daukar matakan da suka dace yayin da take kokarin shawo kan annobar, tana mai cewa, "Muna ganin cewa, gwamnatin kasar Sin tana daukar matakan da suka dace, dalilin da yasa haka shine domin kwayar cutar corona sabuwar kwayar cuta ne da ba a taba ganota ba a baya, saurin yaduwarta yana kawowa babban tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin, haka kuma yana kawowa tasiri mai tsanani ga tattalin arzikin duniya baki daya, kana daga bayanan da muka samu yanzu, muna dauka cewa, matakan da gwamnatin kasar Sin take dauka sun dace da yanayin da kasar take ciki yanzu."

Madam Georgieva ta ci gaba da cewa, gwamnatin kasar Sin ta dauki hadaddun matakai a yankunan da suka fi shan wahalar yaduwar annobar, kuma tana kokarin musanyar bayanan da bangarorin da abin ya shafa da hukumar lafiya ta duniya wato WHO da sauran kasashenn duniya, a don haka asusun bada lamuni na duniya ya nuna yabo gare ta, a cewarta: "Mun lura cewa, gwamnatin kasar Sin ta dauki hadaddun matakai a yankunan da suka fi shan wahalar yaduwar annobar cikin sauri, domin tabbatar da hidimar kiwon lafiyar jama'a a wuraren, kana ta kara karfafa cudanyar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya a bangaren tasirin da annobar take kawowa kasa da kasa, hakika na yi farin cikin ganin kasar Sin ta yi musanyar bayanai da WHO, haka kuma na yi farin cikin ganin kasar Sin ta sanar da bayanan da abin ya shafa ga kasashen duniya a kan lokaci, saboda hakan zai taimakawa al'ummomin kasashen duniya su kara fahimtar hakikanin yanayin yaduwar annobar cikin lokaci."

Kana madam Georgieva ta nuna maraba ga matakan yakini a jere da babban bankin kasar Sin ya dauka a kwanakin baya, inda ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta kebe isassun kudade domin dakile yaduwar annobar a kan lokaci, haka kuma ba ta fitar da manufofin sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki a halin yanzu, saboda lokaci bai yi ba tukuna, sai dai bayan da aka tantance tasirin da annobar zata kawowa tattalin arzikin kasar.

Ta kara da cewa, manufofin kasar Sin suna da muhimmanci matuka ga zaman karko na tattalin arzikin kasar Sin, da kuma tattalin arzikin duniya, asusun bada lamuni na duniya yana maida hankali sosai kan batun, zai samar da taimako ga kasar Sin ta hanyoyi daban daban a koda yaushe.

Madam Georgieva ta ce, yanzu kamfanonin kasar Sin sun fara aiki a kai a kai, shi yasa lokaci bai yi ba a tantance tasirin da annobar ta kawowa tattalin arzikin kasar Sin yanzu, tana mai cewa, "Yanzu bai dace ba mu tantance, ya kamata mu yi hasashe, mun yi hasashe cewa, duk da cewa tattalin arzikin kasar Sin ya gamu da matsala, amma zai samu ci gaba cikin sauri, bari mu jira har tsawon mako guda ko kwanaki goma, ya zuwa wancan lokaci, bari mu tantance gudanuwar tattalin arzikin kasar Sin."

Madam Georgieva ta yi nuni da cewa, bayan da aka kawo karshen annobar, za a iya daukar matakan sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki, domin sassauta tasirin da annobar ta kawowa tattalin arzikin kasar ta Sin. Ta ce, "Tasirin da annobar zata kawowa tattalin arzikin kasar Sin yana da nasaba da saurin shawo kan ta, haka kuma yana shafar matakan da gwamnatin kasar zata dauka domin ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar, amma idan ana son tabbatar da burin, dole ne a kara fahimtar yanayin da ake ciki, wato wadannan bangarorin da suke shan wahalar yaduwar annobar, da kuma yadda za a dauki matakan da suka dace domin dakile tasirin."

Madam Georgieva ta jaddada cewa, wasu suna ganin cewa, cutar numfashin ta yi kama da annobar SARS ta shekarar 2003, amma hakika akwai bambanci matuka tsakaninsu, kuma tattalin arzikin kasar Sin da tattalin arzikin duniya da cudanyar dake tsakanin tattalin arzikin kasashen duniya sun samu manyan sauye-sauye a cikin 'yan shekarun da suka gabata, ya dace a maida hankali yayin da ake tantance tasirin annobar kan tattalin arziki.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China