Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Unguwanni na kara zama ginshiki a kokarin da Sin ke yi na shawo kan cutar coronavirus
2020-02-12 20:45:33        cri

Babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar, Mr. Xi Jinping ya jaddada cewa, unguwanni su ne ginshiki a kokarin da Sin ke yi na shawo kan cutar coronavirus. Shugaban ya bayyana hakan ne, a yayin da yake duba yadda ake gudanar da ayyukan kandagarki, da dakile cutar numfashi da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa a kwanan baya a birnin Beijing, babban birnin kasar Sin.

Ya ce, ya kamata unguwannin sassa daban daban na kasar, su taka rawar da ta wajaba a wajen dakile cutar, kuma a sanya su zama ginshiki na aikin shawo kan cutar. Furucin nasa dai, ya bayyana rawar musamman da unguwanni ke takawa a kasar Sin, baya haka kuma, ya nuna alkiblar da za a bi a gaba, wajen gudanar da ayyukan shawo kan cutar.

A halin yanzu, ana gudanar da binciken da ba a taba ganin irinsa ba, a unguwannin birnin Wuhan na lardin Hubei, birnin da cutar ta fi kamari, inda kowace rana jami'ai sama da dubu 30 na unguwanni daban daban, suke kokarin tabbatar da matakan kandagarki ga kowane gida, da ma kowane mutum.

A birnin Beijing, an kuma tura ma'aikatan gwamnati sama da dubu 50 zuwa unguwanni daban daban, don su shiga ayyukan kandagarki na unguwannin.

Abin lura shi ne, a yayin da ake daukar tsauraran matakai na kandagarkin cutar, unguwannin sassa daban daban na kasar Sin, sun kuma dau matakai da dama na samar da tabbaci ga rayuwar al'umma ta yau da kullum, musamman saboda yadda ake bukatar mazauna su zauna a gida a maimakon fita waje a kullum. Misali, wasu unguwanni sun hada gwiwa da kamfanonin saida kayayyaki ta yanar gizo, don taimakawa mazaunansu sayen kayayyaki. Ma'aikatan wasu unguwannin kuma, suna taimakawa mazauna unguwannin wajen sayen kayayyakin da suke bukata, matakan da suka shaida manufar mai da al'umma a gaban komai, da kuma yadda unguwannin suke tabbatar da manufofin gwamnati.

Kamar yadda ministan kiwon lafiya na kasar Afirka ta Kudu Zweli Mkhize ya bayyana, yadda gwamnatin kasar Sin ke ba da jagoranci yadda ya kamata, da yadda al'umma ke amsa kirar gwamnati, da yadda kuma al'ummar kasar ke hada kansu, abubuwa ne masu burgewa. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China