Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin kasar Sin suna iya fuskantar kalubalen dake gabansu
2020-02-10 19:55:52        cri

A kwanan nan, dimbin kamfanonin kasar Sin sun farfado da ayyukansu, kuma majalisar gudanarwar kasar ta bayar da sanarwa, inda ta jaddada muhimmancin daukar matakan kare cutar numfashi da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa, ta yadda kamfanonin za su farfado da ayyukansu yadda ya kamata.

Kamfanoni su ne jigon tattalin arziki, kuma halin da suke ciki, na shaida makomar tattalin arziki. Batun ko ta yaya za a rage illolin da cutar ke haifarwa ga kamfanonin, abun lura ne ga tattalin arzikin kasar Sin a halin yanzu.

A hakika, kamfanoni daban daban na kasar suna iyakacin kokarinsu na farfado da ayyukansu, a yayin da kuma suke kokarin daukar matakan kare yaduwar cutar. A sa'i daya kuma, gwamnatin kasar ma na daukar manufofi, na baiwa kamfanonin cikakken goyon baya.

Baya ga haka, kamfanonin kasar Sin na iya tinkarar matsalar da suke fuskanta ne, a sakamakon kyakkyawan yanayin tattalin arzikin kasar, inda karin masana ilmin tattalin arziki na gida da waje suke ganin cewa, duk da illolin da cutar ke haddasawa ga tattalin arzikin kasar Sin, hakan ba zai dade ba, kuma ba zai canza ingancin tattalin arzikin kasar Sin da ma makomarsa ba.

Da yake, akwai babbar kasuwa dake da mutane biliyan 1.4 a kasar Sin, kuma akwai cikakken tsarin masana'antu da kayayyakin more rayuwa masu inganci, da ma kwararrun fasahohi a kasar, wadanda suka kasance ginshikan ci gaban tattalin arzikin kasar, wadanda kuma suke samar da kuzari ga bunkasuwar kamfanonin kasar. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China