Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana da isassun kayayyakin yau da kullum a kasuwanin lardin Hubei
2020-02-10 11:58:28        cri

A yayin taron manema labaru da kwamitin yaki da annobar cutar numfashi na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya a jiya Lahadi, jami'an hukumomin gwamnatin kasar Sin sun bayyana cewa, yanzu, kasuwannin sayar da kayayyakin yau da kullum a lardin Hubei suna gudanar da harkokinsu kamar yadda aka saba, kuma ana da isassun kayayyakin yau da kullum a dakunan adana kayayyaki na lardin. Sakamakon haka, farashin galibin kayayyaki na ta raguwa. A waje daya kuma, gwamnatin birnin Wuhan na kokarin ingiza kafa wasu manyan kasuwanni a tituna.

A lokacin da yake bayyana yanayin da kasuwannin samar da kayayyakin yau da kullum na birnin Wuhan, har ma na lardin Hubei suke ciki, Mr. Wang Bin, mataimakin babban direktan sashen kula da kasuwanni a ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ya bayyana cewa, a 'yan kwanakin baya, kasuwannin sayar da kayayyakin yau da kullum a lardin Hubei suna gudanar da harkokinsu kamar yadda aka saba, kuma ana da isassun kayayyakin yau da kullum a dakunan adana kayayyaki a lardin. Sakamakon haka, farashin galibin kayayyaki yana ta raguwa.

"An bincika yawan shinkafa da taliya da man girki da naman dabbobi da madara da ake da su a dakunan adana su a duk fadin lardin Hubei, an gano cewa, yawansu zai iya tabbatar da biyan bukatun da ake da su cikin kwana 10 zuwa 15 masu zuwa. Sannan yawan naman gabas da kwai da ake da su zai iya biyan bukatun da ake da su cikin kwanaki 5 masu zuwa. Sannan yawan kayan lambu da ake da su zai iya biyan bukatun da ake da su cikin kwanaki 3 masu zuwa. Bugu da kari, yanzu ana ta samar da karin wadannan kayayyakin da ake bukata a kullum. Sakamakon haka, yanzu yanayin samar da isassun wadannan kayayyaki na yau da kullum ga birnin Wuhan ya samu kyautatuwa."

An kuma labarta cewa, gwamnatin birnin Wuhan tana kokarin ingiza kafa wasu manyan kasuwannin sayar da kayan lambu a kan tituna. Ya zuwa ranar 8 ga wata, an riga an kafa manyan kasuwanni 14 a kan titunan birnin Wuhan. Mr. Wang Bin ya kara da cewa, "A cikin 'yan kwanakin nan, an fara sayar da dankalin Turawa da karas da albasa da ake bukata a kullum da sauran kayayyakin lambu da mazauna birnin Wuhan suke son saye. An shigar da galibin wadannan kayayyakin lambu daga sassa daban-daban na kasar Sin, a yayin da wasu 'yan kasuwa suka shigar da wasu kayayyakin lambu daga hannun manoma wadanda ke zaune a yankunan karkarar birnin Wuhan. Fadin wadannan manyan kasuwanni suna da girma, yanzu mazauna wadanda ke zaune a unguwannin dake kusa da su, sun fi son sayen wadannan kayayyakin yau da kullum a wadannan manyan kasuwanni."

A halin da ake ciki yanzu kuwa, ana da isassun kayayyakin yau da kullum iri daban daban a dukkan kasuwannin kasar Sin, kuma farashinsu bai hau sosai ba. Mr. Chen Da, mataimakin babban direktan sashen kula da tattalin arziki da cinikayya na kwamitin raya kasa da yin gyare-gyare na kasar Sin ya bayyana cewa, an dauki matakan kara sa ido kan yadda ake gaggauta samar da muhimman kayayyakin da ake bukata a kasuwa a kullum, da kuma yadda kamfanoni da masana'antu suke hanzarta samar da kayayyaki, musamman kara karfin tabbatar da samar da muhimman kayayyakin yau da kullum a kasuwa, da kuma cika dakunan adana kayayyaki domin tabbatar da samar da isassun kayayyaki a duk fadin kasar. Mr. Chen Da yana mai cewa, "Bisa kididdigar da aka bayar a baya bayan nan, a ranar 8 ga watan Faburairu, farashin shinkafa da na garin alkama da na man girki da ake sayarwa a manya da matsakaitan birane 36 na fadin kasar Sin ya yi kusan daidai da na wata daya da ya gabata. Farashin kwai ya ragu kadan, sannan farashin kayayyakin lambu iri 15 ya ragu da kashi 10 cikin dari bisa na ranar 30 ga watan Janairu. An yi hasashen cewa, za a iya tabbatar da isassun muhimman kayayyakin yau da kullum da ake bukata a duk fadin kasar Sin, ciki har da birnin Wuhan, kuma farashinsu ma ba zai hau sosai ba."

An kuma bayyana cewa, kwamitin raya kasa da yin gyare-gyare na kasar Sin zai hada hannu da sauran hukumomin gwamnatin kasar wajen kyautata aikin sa ido kan kasuwa, da tabbatar da samar da karin kayayyakin yau da kullum a kasuwa, da kuma kara daidaita karfin sufurin su kamar yadda ake fata, ta yadda za a iya biyan karin bukatun da ake da su a wasu manya da matsakaitan birane sakamakon dawowar ma'aikata daga sassa daban daban na kasar. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China