Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda kasar Sin ke kokarin dakile yaduwar cutar numfashi ya shaida yadda take sauke nauyin da ke bisa wuyanta
2020-02-06 12:36:19        cri

Dangane da jerin matakan da gwamnatin kasar Sin take dauka na kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa, kwanan nan, babban editan jaridar Akhbarelyom ta kasar Masar, Gamal Hussain ya bayyana cewa, yadda kasar Sin ke daukar kwararan matakai na tinkarar cutar ya shaida ingancin aikin gwamnati da kuma hadin kan al'ummar kasar.

A kwanakin baya, rahotannin da kafofin yada labarai na kasar Sin suka bayar dangane da cutar numfashi wanda kwayar cutar coronavirus ke haddasawa sun janyo hankalinsa. A ganinsa, duk da cewa yawan girman filaye na kasar da al'ummarta masu dimbin yawa sun karawa kasar wahalar aikin shawo kan cutar, amma matakan da gwamnatin kasar ta dauka ba tare da bata lokaci ba sun dakile karin yaduwar cutar. Ya ce,

"Kasar Sin ta dauki kwararan matakai masu inganci, wadanda suka samu amincewa daga hukumar lafiya ta duniya(WHO). Idan mun yi nazari kan halin da ake ciki yanzu, za mu gane cewa, hakarta tana cimma ruwa, kuma muna sa ran kasar Sin za ta kara cimma nasarori nan ba da jimawa ba."

 

Gamal Hussain, ya taba ziyartar biranen Beijing da Guangzhou na kasar Sin, don haka, yana sane da ayyukan more rayuwa na kasar. Ya ce, daga cikin matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka na dakile yaduwar cutar, abin da ya fi burge shi shi ne yadda aka gina wasu asibitoci na wucin gadi a birnin Wuhan cikin saurin gaske. Ya ce,

"Sin babbar kasa ce mai tasowa, wadda kuma kasa ce da ta kware wajen raya ayyukan more rayuwa. Yadda kasar Sin ta sanar da gina wasu manyan asibitoci biyu na karbar masu cutar cikin wasu kwanaki kalilan ya jawo hankalin al'ummar duniya. Babu shakka, wannan aiki ne a zo a gani da kasar ta gudanar a kokarinta na dakile yaduwar cutar, wanda ya shaida niyyar al'ummar kasar da hadin kansu, da kuma yadda kasar ta sauke nauyinta na shawo kan cutar."

Gamal Hussain ya kara da cewa, bullar cutar ta sa kasa da kasa sun zurfafa tunani a kan hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar kiwon lafiya, kuma a halin da ake ciki, Masar na fatan koyon fasahohi daga kasar Sin, don a inganta hadin gwiwar kasashen biyu ta fannin kiwon lafiya.

"Kawo yanzu, an gano bullar cutar a kasashe da dama, duk da cewa cutar ba ta shafi Masar ba tukuna, amma gwamnatin kasar tuni ta sanar da daukar matakan kandagarki daga dukkan fannoni. A sa'i daya kuma, kara musayar bayanai a tsakanin kasashen biyu ya kasance wani muhimmin bangare na hadin gwiwarsu a yanayin da ake ciki na tinkarar cutar."

A ranar 1 ga wata, ma'aikatar kiwon lafiya da al'umma ta kasar Masar ta sanar cewa, za ta samar da gudummawar kayayyakin kiwon lafiya kimanin ton 10 ga kasar Sin, don taimaka mata wajen shawo kan cutar. A game da wannan, Mr. Gamal ya ce, "Zumuncin da aka kulla a lokacin da ake cikin mawuyacin hali zumunci ne na gaske", kuma Masar na fatan ganin gwamnatin kasar Sin da al'ummarta za su samu galabar yaki da cutar. Ya ce,

"Bayan bullar cutar, gwamnatin Masar da al'ummarta na maida hankali sosai kan kasar Sin. Kasashen biyu suna da dadadden zumunci, kuma gwamnatin Masar ta samar da gudummawarta ne a sakamakon yadda kasar Sin ta dade da samar da nata gudummawar. A ganina, zumuncin da aka kulla a lokacin da ake cikin mawuyacin hali zumunci ne na gaske. Da sahihin zuci ne nake fatan kasar Sin za ta shawo kan matsalar cikin sauri kuma ba tare da fuskantar mummunar hasara ba. Ina gaskanta cewa, kasa da kasa, ciki har da Masar, za mu hada kai da kasar Sin, domin dakile cutar."(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China