Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Kara Kokarin Aiwatar Da Matakan Da Aka Dauka Don Cimma Nasarar Dakile Annobar
2020-02-05 20:13:57        cri

An kira taron zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) a kwanan baya, inda manyan shugabannin kasar suka tattauna ayyukan tinkarar cutar numfashi mai yaduwa ta Novel Coronavirus. Babban magatakardan kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS, Xi Jinping shi ne ya jagoranci taron, gami da gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya ce yanzu batu dake da matukar muhimmanci shi ne a yi kokarin aiwatar da dukkan matakan da aka tsara. Maganarsa ita ce sabon umarnin da shugaban kasar Sin ya bayar kan aikin dakile annobar, kuma jagora ga ayyukan da ake gudanarwa don ganin bayan wannan cuta.

Hakika kokarin aiwatar da matakai da manufofi wata nagartacciyar al'ada ce ta jam'iyyar JKS dake jan ragamar mulki, kuma dabara ce mai muhimmanci da kasar Sin ke dauka don neman raya kasar. A wannan lokacin da ake fuskantar yaduwar cutar numfashi, yadda ake kokarin gudanar da ayyuka bisa umarnin shugabannin kasar yana da muhimmanci sosai. Saboda idan har aka aiwatar da matakan da aka tsara yadda ake bukata, hakika za a samu sakamako a kokarin dakile annobar. Ana iya kallon annobar a matsayin wata jarrabawa ga gwamnatin kasar Sin, kan tsarinta na kula da harkokin kasa, da yadda take gudanar da mulki. Ta hanyar aiwatar da dukkan matakan da aka tsara yadda ake bukata, da kyautata salon ayyuka, tabbas kasar Sin za ta yi nasara a wannan yakin da take yi da annobar da ta bulla a kasar. (Mai Fassarawa: Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China