Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dogaro kan karfin jama'a domin dakile yaduwar cutar coronavirus
2020-01-30 21:55:11        cri

Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice ya gabatar da wani sharhi yau Alhamis, mai taken "Dogaro kan karfin al'umma domin dakile yaduwar cutar coronavirus". Sharhin ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, a lokacin da ake kokarin kandagarkin yaduwar cutar numfashin da kwayar cutar coronavirus ke haifarwa, ya zama dole a maida muradun jama'a a gaban kome, domin samun galaba kan yaki da cutar bisa dogaro kan karfin jama'a baki daya.

Sharhin ya nuna cewa, maida moriyar al'umma a gaban kome da kuma dogara ga karfin jama'a kyakkyawar al'ada ce ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shi ne dalilin da ya sa kasar ta iya samun ci gaba da tsayawa. Kalaman Xi Jinping na nuna wajibci gami da muhimmancin karfafawa daukacin al'ummar kasar gwiwar su shiga a dama da su a ayyukan dakile yaduwar cutar.

Hannu daya ba ya daukar jinka, a cewar malam Bahaushe. A halin yanzu al'ummar kasar Sin sun zama tsintsiya madaurinki guda domin daukar matakan kandagarkin yaduwar wannan cuta. Dukkanin larduna 31 a kasar sun kaddamar da matakan koli domin tinkarar annobar cutar, domin ba da fifiko ga aikin dakile yaduwar cutar. Sa'an nan jami'an gwamnati a matakai daban-daban sun shiga wurare daban-daban domin daukar matakan hana yaduwar cutar, kana ma'aikatan jinya sama da dubu shida sun tafi lardin Hubei domin ba da tallafin gaggawa. Ma'aikata daga sana'o'i daban-daban na himmatuwa wajen samar da kayan bukatun gaggawa ba dare ba rana, masana kimiyya da fasaha su ma suna kokarin nazarin allurar rigakafin wannan cuta. Wannan ya nuna cewa, al'ummar kasar daga bangarori daban-daban na bakin kokarinsu wajen hana yaduwar cutar.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China