Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin da Amurka ta yi ba zai yi tasiri ko kadan ba
2020-01-30 16:39:05        cri

Majalisar wakilan Amurka ta zartas da wani shirin doka kan manufofin yankin Tibet da goyon-bayansu na shekara ta 2019, al'amarin da ya keta dokoki gami da ka'idojin dangantakar kasa da kasa, da aikewa da mummunan sako ga 'yan aware na Tibet. Zartas da dokar ya shaida irin mummunar makarkashiyar da wasu 'yan Amurka suka kulla wajen yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar Sin da kawo illa ga cikakken yankinta ta hanyar amfani da batun da ya shafi Tibet.

Ko da a bangaren tsari ko tarihi ko kuma bisa doka, gwamnatin kasar Sin na da cikakken 'yanci na amincewa da tsarin gado na addinin Buddah a yankin Tibet. A zahiri ma, ko shi Dalai Lama na 14 ya gaji wannan matsayi ne bisa tsarin addinin Buddah wanda kuma ya samu amincewa daga gwamnatin kasar. Amma yanzu, shirin dokar da majalisar wakilan Amurka ta zartas ta tsoma baki cikin harkokin tsarin gado na addinin Buddah na Tibet, kuma wannan al'amari ne da ya lalata al'adar addinin Buddah, kana katsalandan ne babba cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma ya sabawa doka.

Har wa yau, shirin dokar ya sake ambato batun da ya shafi kafa ofishin jakadancin Amurka a Lhasa, fadar mulkin jihar Tibet, inda ta yi barazanar cewa, idan kasar Sin ba ta yarda ba, Amurka ba za ta amince ta kafa sabbin ofisoshin jakadancinta a kasar ba. Wannan ya sake bayyana irin girman kai da wasu Amurkawa ke nunawa, gami da makircinsu na yin shiga sharo ba shanu cikin batun yankin Tibet da kawo baraka ga kasar ta Sin.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China