Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG ya gabatar da shirye-shiryen bikin bazara masu kayatarwa domin murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta al'ummar kasar Sin
2020-01-25 00:04:29        cri



Yau Jumma'a ita ce jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta al'ummar kasar Sin, wato shekara ta bera, inda a yammacin yau babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice ya gabatar da wani kasaitaccen bikin kade-kade da raye-raye domin taya al'ummar kasar murna, wanda ke kunshe da nagartattun al'adu gami da fasahohin zamani, ciki har da fasahar sadarwar 5G da kuma jirage marasa matuka.

Bikin na tsawon minti 260 ya kunshi shirye-shirye masu kyau da dama, ciki har da kade-kade da raye-raye, da wasan dabo, da wasan lankwasa jiki wato acrobatics a Turance, da wasannin kwaikwayon gargajiya da sauransu. Shirye-shiryen bikin ya maida hankali sosai kan zamanin da muke ciki da kuma batutuwan da suka jawo hankalin jama'a, akwai na gargajiya akwai kuma na zamani, wadanda suke nuna kauna ga iyaye da dangogi, da nuna kishin kasa, da kokarin cimma buri da nuna fatan alheri ga kasa da makamantansu. Baya ga haka, akwai wani shiri mai suna "kaunar juna" da aka saka a cikin bikin, dangane da yadda ake yaki da cutar numfashi da ta bulla, don ba wa wadanda ke fama da cutar kwarin gwiwa.

A bikin na bana an yi amfani da fasahohin zamani, ta yadda masu kallon shirin za su kasance tamkar suna wajen bikin. A sa'i daya kuma, an yi amfani da mutum mutumin inji da jirage marasa matuki wajen daukar shirin. A takaice dai, kirkire-kirkiren fasahohi sun samar da sabbin fasahohi masu yawa ga bikin na wannan shekara.

Baya ga dandalin bikin da aka kafa a birnin Beijing, an kuma kafa wasu rassa biyu na bikin a birnin Zhengzhou da kuma babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao, abin da ya nuna mana al'adun sassa daban daban na kasar Sin. An watsa shirin bikin ne ta kafofi daban daban, kuma an gabatar da shi ne kai tsaye ga duniya baki daya.

A yayin bikin na bana, CMG zai kuma tsara tare da gabatar da fim din bikin kade-kade da raye-raye na murnar shiga sabuwar shekara ta gargajiya ta kasar Sin a gidajen sinima. Kafofin watsa labaru sama da 500 na kasashe da shiyyoyi sama da 170, ciki har da Amurka, Burtaniya, Japan, Rasha, Brazil, Singapore, Hadaddiyar daular Larabawa, Malaysia, Thailand, Laos da dai sauransu, kana da gidajen sinima na kasashe da shiyyoyi fiye da 20 za su watsa fim din shirye-shiryen bikin murnar shiga sabuwar shekara.

An fara shirya bikin murnar shiga sabuwar shekara ta gargajiyar kasar Sin a shekarar 1983, wannan wani gaggarumin biki ne da gidan talibijin na kasar Sin ya gabatar a gabannin ranar sabuwar shekara bisa kalandar gargejiyar kasar. A shekaru 30 da suka wuce, bikin ya riga ya kasance shirin da ya fi jawo hankulan masu kallo a duniya bisa matsayin bajintar duniya na Guinness. Bikin ya riga ya zama wani bangare ne na al'adar gargajiya ta jama'ar kasar a jajibirin sabuwar shekara.(Masu fassara:Murtala Zhang, Lubabatu Lei, Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China