Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tabbas Sin za ta shawo kan cutar numfashin da ta bulla
2020-01-22 20:38:32        cri

Gwamnatin kasar Sin tana kokari matuka domin shawo kan annobar cutar numfashi da ta barke a birnin Wuhan na lardin Hubei na kasar Sin, wadda a halin yanzu ta ke kara kawo bazuwa, domin kiyaye lafiyar jama'a. Haka kuma gwamnati tana kara yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya, ta yadda za a hana bazuwarta, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana sauke nauyin dake bisa wuyanta na kiyaye lafiyar jama'a a fadin duniya.

Tun bayan da aka samu rahoton bullar cutar numfashi a birnin Wuhan a ranar 30 ga watan Disambar bara, nan take gwamnatin kasar Sin ta tura kwararru zuwa birnin domin ba da taimako da goyon bayan da ya dace don shawo kan annobar cikin lokaci, daga baya an gano dalilin da ya sa aka kamu da cutar a cikin mako guda daya kawai, wannan ya samar da sharadi da lokaci ga aikin shawo kan cutar. Domin gudanar da aikin yadda ya kamata, gwamnatin kasar Sin tana ba da bayanai da rahotanni game da annobar cikin lokaci, haka kuma ta yi cudanya da kungiyar kiwon lafiya ta duniya, tare kuma da sanar da bayanai ga kasashen da abin ya shafa da yankunan Hong Kong da Macao da kuma Taiwan a kan lokaci.

Darektan sashen nazarin cututtuka masu bazuwa na kwalejin koyar da ilmin lokitanci ta jami'ar Harvard ta Amurka Eric Rubin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakin da ya dace a kokarin shawo kan cutar numfashin, bayanan da ta samar sun taimaka matuka wajen dakile annobar a fadin duniya.

Duk da cewa ana kara fuskantar cututtuka masu bazuwa da dama yanzu, amma karfin dakile cututtuka dake shafar bil Adama shi ma ya dagu, a don haka bai bukata jama'a su ji tsoro ba, gwamnatin kasar Sin da al'ummun kasar suna cike da imani kan aikin shawo kan sabuwar cutar numfashin saboda ta riga ta kafa wani cikakken tsarin magance da shawo kan annobar da ta barke cikin gaggawa tun bayan shekarar 2003, lokacin da aka gamu da annobar SARS, ko murar H1N1.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China