Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan wasan kasar Sin masu tseren gudun Marathon sun samu horo a Kenya
2020-01-22 14:09:41        cri

Ana yiwa Eldoret na kasar Kenya lakabi da "Garin gudun Marathon". A karshen shekarar 2019, kungiyar 'yan wasan gudun dogon zango wato Marathon ta isa garin domin samun horo, don share fagen wasan fid da kwararru na gasar wasan Olympics da za a yi a Tokyo a watan Maris mai zuwa. Mamban kungiyar Dong Guojian yana sa ran zama matsayi na 8, da kuma karya matsayin bajinta na kasar Sin a cikin gasar wasan Olympics ta Tokyo.

Da karfe 5 na sanyin sassafe akwai sauran duhu a Eldoret, amma Dong Guojian da abokansa sun tashi da wuri sun fara horo. Yau za su yi horo tare da 'yan wasa na Kenya. Dong Guojian ya ce:

"Horo da muke yi yau, horo ne na Fatlek na awa daya, 'yan wasa na Kenya suna da kwarewa matuka, mun koyi abubuwa da dama daga wajensu, kuma mun samu ci gaba sosai."

Yanayin horon na da bambanci sosai tsakanin Sin da Kenya. A Eldoret dai akwai rairayi a kan hanya. An iya ratsa hanyoyi dake kewaye da ciyayi, filin kiwon dabbobi da itatuwa irin na Afirka.

A cikin horon da aka yi, Dong Guojian da abokinsa Peng Jianhua na sahun gaba, kuma a gabansu dan wasa mai suna Eliud Kipchoge ne, wanda ya karya matsayin bajintar kammala wasan Marathon cikin awo'i 2. Bayan horo, Dong Guojian ya ce:

"Mun gama horo a yau, ko wacce Talata, Alhamis da Asabar, muna yin horo tare da Kipchoge, akwai gibi a tsakaninmu, hakan ya sa muke shan wahala a yayin horon."

Eldoret na da tsayin mita 2400 zuwa 2600, hali ne mai kyau ga masu wasan Marathon. Ban da wannan kuma, ko da yake, ana fuskantar yanayi mai wuya a wurin, amma hakan na da kyau ga horo.

A cikin shekarun baya-bayan nan, 'yan wasan kasar Sin su kan samu horo a Kenya, sun samu ci gaba mai armashi. Dong Guojian da Peng Jianhua sun samu horo a Kenya sau da dama. Ban da tsayin Eldoret mai dacewa da yanayi mai wuya da ake fuskanta, kwararru masu dimbin yawa a wannan fanni da Kenya ke da su, sun zama babban dalili na jawo hankalin 'yan wasan kasar Sin. Peng Jianhua ya ce:

"Yanayi a wurin na da bambanci sosai da kasar Sin, ni kadai ina horo a gida, amma a Kenya ina samun horo da wadannan kwararru, kuma hakan na yi min matsin lamba sosai."

'Yan wasan Marathon 11 na cikin wannan kungiya a wannan karo, maza 5 da mata 6 ne. Daga cikinsu, Dong Guojian da Peng Jianhua sun fi kwarewa, suna cikin 'yan wasa da suka kammala gasar gudun Marathon a cikin awo'i 2 da mintoci 10 a shekarar 2019. Ban da wannan kuma, Dong Guojian ya kai ga sabon matsayi a rukunin maza a cikin shekaru 12 da suka gabata.

Kafin wannan kuma, 'yan wasan ba su taba samun maki mai kyau a wannan fanni ba, matsayi mafi kyau da aka samu shi ne na 26 kacal. Dong Guojian ya ce, bayan samun horo a Kenya, an samu maki mai kyau a Berlin. Karo na uku ke nan da Dong zai shiga wasan Olympic, yana kuma sa ran samun maki mai kyau, da karya matsayin bajintar kasar Sin a wannan fanni.

Ban da wannan kuma, 'yan wasan kasar Sin sun samu maraba sosai daga 'yan wasan Kenya. Kipchoge ya ce, Sin na shirya gasanni fiye da 1100 a ko wace shekara, don haka za ta zama kasa mafi karfi a wannan fanni. Yana matukar maraba da 'yan wasan kasar Sin, da samun horo a kasarsa, don kara azama kan bunkasuwar Marathon. Ya ce:

"Yanzu babu mutane da dama a kasar Sin da suke wasan gudun dogon zango ko Marathon, hakan ya sa, ake bukatar dogon lokaci don horar da kwararru dake matsayin koli da dama a wannan fanni. Ina fatan 'yan wasan kasar Sin za su kara shiga wannan wasa, don kara azama kan bunkasuwar wannnan wasa a kasar Sin cikin sauri." (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China