Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya dace a kara habaka cudanyar tattalin arzikin duniya
2020-01-21 19:07:50        cri

A yau Talata 21 ga watan nan ne, aka kaddamar da dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya a Davos na Switzerland, inda aka kara mai da hankali kan batun cudanyar tattalin arzikin duniya.

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada, yayin da ya gabatar da muhimmin jawabi shekaru uku da suka wuce, a halin da ake ciki yanzu, ba zai yiwu a katse huldar dake tsakanin kasa da kasa a bangarorin zuba jari, da fasaha, da samar da kayayyaki, da sana'o'i da musanyar kwararru ba.

Dalilin da ya sa aka samu koma baya, yayin da ake kokarin habaka cudanyar tattalin arzikin duniya shi ne, wasu kasashe suna dauka cewa, ba su samu moriyar da ta dace ba, kana abu mafi muhimmanci shi ne tattalin arzikin duniya bai samu ci gaba yadda ya kamata ba, hakan ya sa kasashe masu ci gaba, da kuma kasashe masu tasowa, dukkansu suka gamu da matsin lamba.

Kafin shekaru uku da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taba gabatar da dabarun daidaita wannan matsala a fannoni hudu, wato nacewa ga manufar yin kirkire-kirkire, domin ciyar da tattalin arziki gaba, da nacewa ga manufar hada kai domin gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa mai salon bude kofa, da nacewa ga manufar raya kasa bisa bukatun sabon zamanin da ake ciki, domin tsara dabarun gudanar da harkokin kasa bisa adalci, da nacewa ga manufar adalci, da hakurin juna, domin samun ci gaba tare, dabarun da suke ci gaba da taka rawar gani a fannin ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

Babban taken taron shekara na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na bana shi ne, "Hada kan daukacin kasashen duniya, domin cimma burin samun dauwamammen ci gaba", saboda kara habaka cudanyar tattalin arzikin duniya, sabbin bukatun ci gaban tarihi ne a halin yanzu. Duk da cewa, kila a samu koma baya a wasu lokuta, amma ba zai yi yiwu a hana wannan yunkuri ba. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China