Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samar da sabon karfin inganta 'yan uwantakar da ke tsakanin Sin da Myanmar
2020-01-18 20:33:37        cri

A yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke zantawa da takwaransa na kasar Myanmar, U Win Myint a jiya Jumma'a a birnin Naypyidaw, fadar mulkin kasar Myanmar, ya bayyana fatansa na isar da sakwanni uku ta wannan ziyarar tasa, ciki har da nuna goyon baya ga gwamnatin Myanmar da al'ummarta wajen bin hanyar neman ci gaba da ta dace da yanayin kasar, da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakanin kasashen biyu, da kuma ingiza hadin gwiwar da ke tsakaninsu, furucin da ya bayyana tsayayyen goyon bayan da kasar Sin ke nuna wa Myanmar a kokarinta na neman ci gaba, wanda kuma ya samar da sabon karfi ga inganta 'yan uwantakar da ke tsakaninsu.

Abin lura shi ne, a yayin da shugaba Xi Jinping ke zantawa da takwaransa na Myanmar, ya jaddada cewa, Sin ba ta taba tilasta wa wata kasa hada gwiwa da ita ba, kuma ba ta taba tsoma baki cikin harkokin gidan wata kasa ba. Lamarin da ya shaida cewa, manufar diplomasiyya ta kasar Sin ce ta zauna lafiya da kasa da kasa tare da aiwatar da hadin gwiwar samun moriyar juna. A sabo da haka, shugaba U Win Myint cewa ya yi kasar Sin ta samar da taimako ba tare da son kai ba ga ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma a Myanmar, kuma ita Myanmar za ta tsaya ga manufar kasar Sin daya tak a duniya, tare da martaba manufar kasa daya mai tsarin mulki biyu da ta dauka a yankunan Hong Kong da Macao, kuma kullum tana ganin Taiwan a matsayin wani yankin da ba za a iya raba shi daga kasar Sin ba, tana kuma son gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakanin kasashen biyu.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China