Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar kwastam ta Sin ta ba da iznin shigo da abinci da amfanin gona iri 77 na kasashe da yankuna guda 82
2020-01-17 14:19:30        cri

Jiya Alhamis, babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fidda bayanin cewa, a shekarar 2019, gaba daya, hukumar ta karba tare da binciken kararrakin fasa kwauri guda 4198, sa'an nan, ta ba da iznin shigo da abinci da amfani gona iri 77 na kasashe da yankuna guda 82, lamarin da ya taimaka matuka wajen biyan bukatun al'umma da kuma daidaita farashin kayayyaki. Wani jami'i a babbar hukumar kwastan ta kasar Sin ya bayyana cewa, a shekarar 2020, hukumar za ta ci gaba da yaki da masu fasa kwauri, da inganta bunkasuwar tattalin arziki mai inganci.

Cikin dukkanin kararrakin fasa kwauri da hukumar kwastan ta kasar Sin ta bincike a shekarar 2019, kusan rabi daga cikinsu kararraki ne dake shafar batun haraji, kuma darajar kayayyakin da suka shafa ta kai kudin RMB biliyan 78.16, adadin da ya karu da 74.3%.

Bincike ya nuna cewa, an yi nasarar hana shigo da bolar da kasashen waje suke neman jibgewa a cikin kasar. A shekarar 2019, babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta bincike karar fasa kwaurin bolar da kasashen waje suke jibgewa a kasar guda 372, adadin da ya ragu da 22.7% bisa makamancin lokacin bara. Yayin da nauyin bolar ya kai tan dubu 762, wanda ya ragu da 50.9%.

A jawabin da shugaban babbar hukumar kwastam ta kasar Sin Ni Yuefeng ya yi a ranar 16 ga wata, game da ayyukan hukumomin kwastam na kasar Sin na shekarar 2020, ya ce, "Sakamakon kammala aikin sharewa da mayar da bola masu kwari, da inganta aikin aiwatar da dokoki cikin hadin gwiwar kasa da kasa bisa taken "kare kyakkyawar duniyarmu", mun cimma nasarar hana shigo da bolar daga kasashen waje, lamarin da ya samu amincewar kasa da kasa. Mun kuma dukufa wajen yaki da masu fasa kwaurin hauren giwaye da sauran kayayyakin da aka kere da halittu dake fuskantar barazanar karewa baki daya a doron kasa, a dukkan fannoni da kuma hanyoyi iri daban daban, domin gudanar da bincike kan batun yadda ya kamata."

A shekarar 2019 da ta gabata, hukumar kwastam ta kasar Sin ta gudanar da bincike kan karar fasa kwaurin kayayyakin da aka samar da hauren giwaye guda 170, ta kuma karfafa hadin gwiwarta da kasashe da yankuna da ma kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa kan batun, ta kuma taimakawa hukumar kwastam ta yankin Hong Kong na kasar Sin, da hukumomin kwastam na kasashen Malaysia, Vietnam da Singapore wajen binciken kayayyakin hauren giwaye sama da ton 11 da aka yi sumogan su, da hauren karkanda sama da kilo 106 da dai sauransu.

A shekarar 2019, hukumar kwastam ta kasar Sin ta mai da hankali kan yaki da fasa kwaurin motoci, da na'urorin wutar lantarki, da kayayyaki masu daraja da dai sauransu, kuma ta gudanar da bincike kan karar fasa kwauri da darajar su ta kai yuan sama da miliyan 10 guda 270, adadin da ya karu da 55.2%.

Ban da haka kuma, a fannin kyautata yanayin kasuwanci, hukumar kwastam ta kasar Sin ta dukufa wajen inganta ayyukan dake shafar shiga da fice, domin rage lokaci da kudaden da aka kashewa a wannan fanni. Ni Yuefeng ya ce, "Idan aka kwatanta da na shekarar 2017, za a ga cewa, lokacin da aka kashe wajen shigo da kayayyakin ya ragu da 62.3%, yayin da lokacin fitar da kayayyakin shi ma ya ragu da 78.6%. An kuma fara gudanar da bincike kan iznin shigi da fice na tsaron abinci guda biyu a bangaren hukumar kwastam, da soke iznin shigo da na'urorin wutar lantarki guda 118. Kuma kudin hidima kan ayyukan shigi da fice ya ragu sosai."

A shekarar 2019 kuma, hukumar kwastam ta kasar Sin ta ba da gudummawa kan kyautata yanayin cinikin kasa da kasa, da goyon bayan cinikin dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake iyaka da ita, da bude hanyar cinikin amfanin gona mai sauki a tsakanin kasar Sin da kasar Vitenam da kuma kasar Kazakhstan da dai sauransu. bugu da kari, hukumar kwastam ta kasar Sin ta kafa tsarin kididdiga da bincike kan mayar da kayayyaki a tsakanin 'yan kasuwa dake amfani da yanar gizo a tsakanin kasar Sin da kasashen ketare, ta kuma dauki matakai da dama domin habaka shigo da hatsi da nama da dai sauransu, ta kuma ba da iznin shigo da abinci da amfanin gona iri 77 ga kasashe da yankuna guda 82, lamarin da ya ba da tabbaci kan farashin kayayyaki a kasuwannin kasar Sin, da biyan bukatun al'ummar kasar Sin yadda ya kamata.

A shekarar 2020 kuma, Ni Yuefeng ya ce, hukumar kwastam za ta ci gaba da bude kofa ga waje da neman ci gaba mai inganci, da kuma kyautata aikin ba da hidima. Ya ce, "Ya kamata mu dukufa wajen karfafa tsarin dokokin kwastan, da inganta shirye-shiryen kafa dokokin harajin kwastan, kau da bola masu kwari da fasa kwauri da dai sauransu. Haka kuma, za ta zurfafa aikin sabunta tsarin bincike kan yankin ciniki cikin 'yanci na gwaji, da karfafa aikin sa ido kan wasu kayayyakin musamman da suka hada da motoci, kayayyakin jarirai da yara, da sinadarai masu hadari da dai sauransu." (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China