Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin-gwiwar Sin da Afirka za ta amfani duk duniya a sabuwar shekara
2020-01-13 21:35:15        cri

 


A ranekun 7 zuwa 13 ga wata, memban majalissar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya ziyarci wasu kasashen Afirka biyar, ciki hadda Masar, Djibouti, Eritrea, Burundi, da kuma Zimbabwe.

Ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan zabi kasashen Afirka a matsayin ziyararsa ta farko a sabuwar shekara, a shekaru talatin da suka shige, al'amarin da ya zama al'ada a harkokin diflomasiyyar kasar Sin.

Kamar yadda minista Wang Yi ya ce, kasar Sin ba ta taba sauya manufarta kan kasashen Afirka ba, ta kuma dade tana kulla zumunta, da zurfafa hadin-gwiwa tare da kasashen Afirka.

Shekarar da muke ciki, wato 2020, na da ma'ana ta musamman ga kasashen Sin da Afirka, inda a cikin ta ake cika shekaru 20 da kafa dandalin tattauna hadin-gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC a takaice, kana shekara ce ta cika shekaru 60, da kafa huldar jakadanci tsakanin Sin da wasu kasashen Afirka, ciki hadda Ghana da Mali.

An lura cewa, ziyarar da minista Wang Yi ya yi a wannan karo a Afirka, na maida hankali sosai kan tabbatar da matsaya daya da aka cimma tsakanin shugabannin Sin da Afirka, da tabbatar da sakamakon da aka samu, a taron kolin dandalin FOCAC da aka yi a Beijing, da taimakawa ga inganta ayyukan hadin-gwiwa ta fannin shawarar "ziri daya da hanya daya", a wani kokari na kara ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Afirka.

 

A yayin taron kolin Beijing na dandalin tattaunawar FOCAC wanda aka yi a shekara ta 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanar da daukar wasu muhimman matakai takwas, domin karfafa hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wadanda suka jibanci raya masana'antu, da saukaka matakan kasuwanci, da neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kiwon lafiya, da musanyar al'adu, da tsaro da sauransu.

Har wa yau, a bara, kasar Sin ta yi nasarar gudanar da bikin baje-kolin tattalin arziki da kasuwanci na Sin da Afirka karo na farko, inda bangarorin biyu suka yanke shawarar aiwatar da ayyukan hadin-gwiwa sama da 880, nan da shekaru uku masu zuwa.

Tun bayan gudanar da taron kolin Beijing na FOCAC ya zuwa yanzu, sau da dama, manyan jami'an gwamnatin kasar Sin ciki hadda ministan harkokin wajen kasar, sun kai ziyara kasashen Afirka, al'amarin da ya nuna cewa, kasar Sin ta cika alkawarin da ta yi, na zurfafa hadin-gwiwa tare da kasashen Afirka.

A sabon zamanin da muke ciki yanzu, shawarar "ziri daya da hanya daya" da shugaba Xi Jinping ya bullo da ita tana kara taka muhimmiyar rawa. Kawo yanzu, akwai kasashen Afirka 44, gami da kungiyar tarayyar Afirka, wadanda suka rattaba hannu tare da kasar Sin, kan takardar hadin-gwiwa ta shawarar "ziri daya da hanya daya". A bara kuma, jimillar kudin cinikayya tsakanin Sin da Afirka ta zarce dala biliyan 20, har ma Sin ta zama babbar aminiyar kasuwanci ta farko ga kasashen Afirka, a cikin jerin shekaru 11. Yanzu haka kamfanonin kasar Sin sama da 3700, suna zuba jari, da gudanar da kasuwanci a sassa daban-daban na Afirka, domin sanya sabon kuzari ga habakar tattalin arzikin nahiyar.

A ziyarar da ya yi a wannan karo, Wang Yi ya yi takanas inda ya shiga jirgin kasa da ya hada Mombasa da Nairobi, wanda ake kiransa "sabuwar alama ta zumunci tsakanin Sin da Afirka". Haka kuma, shugabanni gami da jami'an gwamnatocin kasashen Kenya, da Djibouti, da Zimbabwe, sun bayyana fatansu na karfafa hadin-gwiwa da kasar Sin ta fannin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya".

Har yanzu dai akwai wasu kasashe 'yan kalilan, wadanda ke kokarin shafawa hadin-gwiwar da ake tsakanin Sin da Afirka kashin kaji. Game da hakan, Mista Wang Yi ya jaddada cewa, yayin da kasar Sin ke hada gwiwa da Afirka, ba ta taba yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba, kuma ba ta taba gindayawa Afirka wani sharadin siyasa ba, inda kawo yanzu, hadin-gwiwar su na kara samar da alfanu ga jama'ar kasashen Afirka.

Idan an dauki tallafin jinya a matsayin misali, za a ga cewa, tun daga shekara ta 1963 ya zuwa yanzu, Sin ta tura ma'aikatan jinyarta sama da dubu 21 ga kasashen Afirka, domin kula da marasa lafiya kimanin miliyan 220, al'amarin da ya samar da babban alheri ga mazauna wurin. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa hadin-gwiwar Sin da Afirka ke samun karbuwa, da amincewa, a kasashen Afirka daban-daban. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China