Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Zimbabwe: Me ya sa Afirka ke maraba da zumuntar kasar Sin?
2020-01-11 18:45:58        cri





Sanin kowa ne cewa, ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin ke kaiwa wasu kasashen Afirka, a duk farkon shekara, ta zama wata al'ada da kasar Sin ta dade tana rayawa. A bana kuma wannan al'ada ke cika shekaru 30 da kafuwa.

A wannan karo, ministan harkokin wajen Sin, kuma dan majalissar gudanarwar kasar Wang Yi, ya fara ziyarar ne a kasashen Masar da Djibouti, da Eritrea, da Burundi da kuma Zimbabwe tun daga ranar 7 ga wata, ziyarar dake dada haskaka irin muhimmanci da Sin ke badawa ga kyakkyawan kawancen ta da kasashen nahiyar Afirka, da ma abota mai inganci dake tsakanin sassan biyu.

A wani bayanin da ya rubuta, gabanin ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin, Mr. Wang Yi zai kai Zimbabwe nan da wasu kwanaki, Ministan harkokin waje da ciniki da kasa da kasa na kasar, Sibusiso Moyo, ya bayyana cewa, Masharhanta na da mabambantan ra'ayi game da moriya da manufar kasar Sin kan kasashen Afirka ko kuma burin da take neman cimmawa. Ya ce wasu na ganin cewa, kasar Sin tana kokarin rage karfin dimokuradiyya a Afirka, a yayin da wasu ke zargin kasar Sin da dora wa kasashen Afirka basusukan da ba su iya biya ba cikin shekaru gommai masu zuwa. Yana mai cewa, mutane kalilan ne suke gaskata cewa, kasar Sin na mai da hankali ne kan moriyar kasashen Afirka, sai dai kusan babu wata kasa da ta tambayi 'yan Afirka ra'ayinsu.

A bayanin da ya rubuta, ministan harkokin waje da ciniki da kasa da kasa na Zimbabwe Sibusiso Moyo ya ce, "ina so in ba da misalin kasarmu ta Zimbabwe, inda muke share fagen ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai kawo mana nan da wasu kwanaki masu zuwa. Ba shakka, kasar Sin kullum ta kasance sahihiyar aminiya ga Zimbabwe."

Ya ce, a karshen shekarun 1970, lokacin da Zimbabwe ke fama da yakin neman 'yancin kanta, kasar Sin ta nuna musu goyon baya mai muhimmanci. Daga karshe, a watan Afrilun shekarar 1980, sun samu 'yancin kai bisa ga 'yancin kada kuri'a da aka tabbatar ga dukkanin 'yan kasar, 'yancin da a baya babu shi ga 'yan Zimbabwe da ke karkashin gwamnatin mulkin mallaka.

Ya kara da cewa, bayan samun 'yancin kai kuma, kullum kasar Sin na ba su ingantaccen goyon baya ta fannonin bunkasa tattalin arziki da ma zaman al'umma.

A hakika, a cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta bi yadda tsarin dokokin MDD ya tanada, ta tsaya ga rashin tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe, kuma abin da take mai da hankali a kai shi ne saukaka harkokin cinikayya da ma zuba jari ga ayyukan more rayuwa da suka wajaba, fannin da ya bai jawo hankalin abokan hadin gwiwarsu ta kasashen yammaci ba har sai shekarun baya bayan nan.

Ya ce, wani abu mai muhimmanci ga huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka shi ne, kasar ta Sin ba ta ko gindaya wani sharadin siyasa ko kuma ba da lacca gare su ba, amma abin bakin ciki shi ne kasashen yamma su kan ba 'yan Afirka taimako bisa sharudan siyasa ko lacca. Wani sharadin da kasashen yamma suka gindaya a bayyane a manufar da suka dauka a kan kasashen Afirka shi ne dole ne mutanen Afirka su karbi ra'ayoyinsu da kuma matakan da suka dauka, duk da cewa ra'ayoyin da matakan ba su dace da al'adu da kuma addinin Afrika ba, lamarin da ya bambanta sosai da manufar kasar Sin a kan kasashen Afirka.

Kasar Sin ba ta neman cin moriya daga kasashen Afirka, kuma a maimakon haka, tana mai da hankalinta sosai a kan kasashen Afirka, musamman ma bayan da aka kaddamar da dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, dandalin dake ta kara samar da damammaki ga kasashen Afirka, wanda har ya sa sauran kasashen duniya su kara zuba jari ga kasashen Afirka.

Ministan ya kara da cewa, Indiya da Koriya ta kudu da Turkiyya da Rasha da dai sauran kasashe bi da bi, sun kafa dandalinsu na hulda da Afirka, dandamalin da ke yunkurin sa kaimin ci gaban kasashen Afirka da ma dunkulewarsu gu daya, a yayin da kuma suke neman damar zuba jari da yin ciniki da kamfanoninsu masu zaman kansu da kuma mallakar gwamnati.

Muhimman abokan hadin gwiwa da suka hada da Amurka da Birtaniya duk sun lura har sun daidaita manufofinsu da suka shafi Afirka, wadanda suka shiga da tallafin bunkasa ayyukan more rayuwa a ciki. Har ma Birtaniya ta sanar da cewa, bayan da ta janye jiki daga kungiyar tarayyar Turai, za ta yi kokarin ganin ta zarce Amurka har ta zama kasar da ta fi yawan zuba jari a Afirka a cikin kungiyar G7.

Wasu na iya ganin cewa, sanarwoyin sun kasance tamkar kalubale ne ga kasar Sin a matsayinta na mafi yawan zuba jari a nahiyar Afirka. Amma Zimbabwe da ma nahiyar Afirka baki daya da kuma kasuwanninsu da ke kara habaka da dunkulewa wuri daya na iya daukar kowane abokin hadin gwiwar da ke neman kulla huldar hadin gwiwar cin moriyar juna da su kamar yadda kasar Sin take yi.

Sai dai aiki ne ja wur ga sabbin zuwa da ma wadanda suka fara gane karfin kasashen Afirka, wato su kai ga matsayin hadin gwiwar da kasar Sin ke yi da kasashen Afirka da ma yawan kudaden da kasar Sin ta zuba ga ayyukan more rayuwa a Afirka. Kasar Sin ta dade da yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, kuma kamar yadda ziyarar da Mr. Wang Yi ta shaida, hadin gwiwar za ta kara fadada.

Ministan ya ce, kwatankwacin abokansu na kasashen yamma, wadanda suke ci gaba da samar da tallafi ga kasashen Afirka bisa haruda. A Zimbabwe, kasashen yamma sun lalata kokarinsu na yin ciniki da zuba jari a kasar bisa ga takunkumin da suka sanya mata, matakin da kuma ya hana kamfanoninsu cin riba a kasar.

Ya ce yayin da suke ganawa da mutanen kasashen yamma, mutanen kasashen yamma su kan bayyana niyyarsu ta kara yin ciniki da zuba jari a Zimbabwe, amma a sa' i daya, wadannan mutane ne su kan kiyaye takunkumin da gwamnatinsu ta sanya wa shugabannin da kuma kamfanonin mallakar gwamnatin Zimbabwe, abu na da wuyar fahimta.

Daga karshe, ministan ya rufe bayanin da cewa, "Don haka, kasancewarta kasar da ke zaman daidaito da mu, wadda kuma ta dade take sada zumunta da mu ba tare da kasala ba, kasar Sin za ta ci gaba da zama kawa ta farko ga Afirka, a sakamakon yadda take fahimta da kuma martaba Afirka." (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China