Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lambar Yabo Mafi Girma A Fannin Kimiyya Ta Bayyana Sirrin Ci Gaba Kimiyya Da Fasahar Sin
2020-01-10 20:12:40        cri

Yau Jumma'a ne, aka yi gagarumin bikin ba da lambobin yabo na kasar Sin a fannin kimiyya da fasaha a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Babban masanin tsara jirgin ruwan yaki na karkashin ruwa mai aiki da makamashin nukiliya na kasar Sin na farko Huang Xuhua, da masanin hasashen yanayin sararin sama Zeng Qingcun sun lashe lambar yabo mafi girma na kasar Sin a fannin kimiyya. Wannan babbar lambar yabo da kasar Sin ta ba su, ta nuna yadda gwamnatin kasar Sin ta girmama masanan kimiyya da fasaha, ta kuma bayyana sirrin yadda kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin kimiyya da fasaha.

Tun lokacin da aka bullo da lambar yabo mafi girma ta kasar Sin a fannin kimiyya a shekarar 1999, ya zuwa yanzu, akwai masana kimiyya da fasaha guda 33 da suka lashe wannan lambar yabo, dukkansu masana ne wadanda suka sami gagarumin ci gaba a fannin kimiyya da fasaha. Kana, sakamakon babban bikin na yau, ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin kimiyya da fasaha ya sake janyo hankulan kasa da kasa

Bari mu ba da misali da shekarar 2019, daga lokacin da na'urar Chang'e-4 ta sauka a bangaren duniyar wata mai nisa, zuwa nasarar harba rokar Changzheng-5, sa'an nan, aka kuma cimma nasarar kirar manhajan kwaikwayon tunanin dan-Adam, dukkansu sun nuna babban ci gaba da kasar Sin ta samu a fannonin kimiyya da fasaha. Masaniya kan batun kirkire-kirkire na kasa da kasa Rebecca Fannin ta bayyana cikin littafinta mai taken "Kwarewar Sin A Fannin Kimiyya Da Fasaha" cewa, kasar Sin tana amfani da bunkasuwar fasahohinta wajen raya harkokin sufuri, kasuwanci, hada-hadar kudi da kiwon lafiya, sadarwa da dai sauransu, lamarin da ya ba da gudummawa ga bunkasuwar kasar baki daya.

Haka zalika, kwanan baya, mujallar kimiya ta kasar Burtaniya ta gabatar da manyan masanan kimiyya da fasaha guda 10 na duniya a shekarar 2019, ciki har da masanin kasar Sin Deng Hongkui bisa nazarin da ya yi a fannin tsarin tantance kwayar halitta na CRISPR. Lamarin da ya nuna ci gaban kasar Sin a fannin raya kimiyya da fasaha.

A yayin da ake karfafa bunkasuwar kimiya da fasahar kirkire-kirkire a duniya, kasar Sin za ta ci gaba da yin kirkire-kirkire da kara bude kofa ga waje da kuma yin hadin gwiwa da kasa da kasa, domin ba da sabuwar gudummawa ga bunkasuwar kasa da kasa da ci gaban bil Adama a fannin kimiyya da fasaha. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China