Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Jianguo: Ya canja rayuwarsa ta hanyar wasannin motsa jiki
2020-01-13 13:15:48        cri

Da karfe 5 na safiyar kowace rana, Wang Jianguo zai fito wurin yawon shakatawa na Renmin na birnin Cangzhou, ya yi wasan tafiya tare da sauran membobin kungiyar wasan tafiya da kafa cikin sauri ta Wanbuyouyue. Su kan yi tafiya a kowace rana, kuma yanayin ruwan sama ko iska ba ya hana su. Wang Jianguo ya kan yin tafiya a can gaban tawagar kungiyar kan kujerar guragu, yana zama kamar wata tutar alama, wadda ke sa kaimi ga sauran membobin kungiyar, da abokan dake kewayensa su shiga su kiyaye yin motsa jiki.

Mamban kungiyar Zhang Dongsheng mai shekaru 60 da haihuwa ya bayyana cewa, "Dan uwa na biyu na kiyaye yin motsa jiki a kowace rana, yanayin iska ko ruwan sama ba ya hana shi. Ya burge ni sosai, ya kamata a maida shi a matsayin misali, mu yi koyi da shi, da kiyaye motsa jiki."

Mambar kungiyar Kan Qinghua mai shekaru 58 da haihuwa ta yabawa halayen Wang Jianguo sosai. Ta ce, "Koda yake Wang Jianguo ya samu nakasa a jiki, amma yana da halaye masu kyau, da tunanin kiyaye samun ci gaba. A kowace rana, yana jagortar mu wajen motsa jiki, mutane da dama suna koyi da shi. Wasu mutane suna da lalaci, ta yadda ba su iya kiyaye motsa jiki, amma ganin shi ya zo, na sawa dukkansu su bi shi, da kiyaye yin motsa jiki tare da shi."

Tsohon mataimakin shugaban kungiyar wasan motsa jiki da wasan tafiya ta kafa cikin sauri ta birnin Cangzhou kuma shugaban kungiyar Wanbuyouyue da Wang Jianguo ke ciki Xu Chunguang ya yi bayani da cewa, an taba bayar da lambar yabo ta "Sarkin wasan tafiya cikin sauri", wato Wang Jianguo ya zama abun misali, tunaninsa ya burge mutanen dake kewayensa sosai, kana ya sa kaimi ga jama'a da su shiga wasan motsa jiki don kiwon lafiya.

Xu Chunguang ya bayyana cewa, "Dan uwa na biyu ya sa kaimi gare mu da mu yi tafiya cikin sauri a kowace rana. Lokacin duk da muka yi tafiya da safe, sai mu ji dadi a dukkan rana. A cewar dan uwa na biyu, yin tafiya da matakai dubu 10, na sawa a ji dadi a zuciya a dukkan rana, da ma jin dadin duk zaman rayuwa. Shi ne sarkin wasan tafiya cikin sauri na kungiyarmu, wato tunaninsa ya burge mu sosai, ya sa mana kaimi na kiyaye yin motsa jiki don kiwon lafiya."

Wang Jianguo ya samu farfadowa a rayuwarsa ta wasanni, da sake tsara sabon burinsa na zaman rayuwa, wanda ya maida zaman rayuwarsa na musamman, da samun darajar rayuwarsa. Kokarin da ya yi a kan wasanni ya shaida tunaninsa na kiyaye samun ci gaba, kana shi ma tunaninsa ya burge mutane da dama dake kewayensa, wadanda su ma suke more darajar da aka samu daga wasannin motsa jiki, tare da kara jin dadin zaman rayuwa.

Wang Jianguo ya bayyana cewa, zai ci gaba da yin motsa jiki a nan gaba. Ya ce, "Ina yin kokari, da neman samun ci gaba yayin da nake halartar gasar wasanni na nakasassu. Ina tsammani, ya kamata na taka wata hanya mai dacewa, idan ban yi kokari ba, ba zan samu kyakkyawan sakamako ba. A nan gaba, zan kiyaye yin motsa jiki, da yin tafiya cikin sauri tare da membobin kungiyar, don ragewa, ko kawar da matsalolin da na kawowa iyali na, da zamantakewar al'umma. Ni ina da tunani mai karfi, ina son ci gaba da yin motsa jiki." (Zainab Zhang)


1  2  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China