Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar dokokin Iraqi ta bukaci gwamnati ta kori dakarun kasashen waje daga kasar
2020-01-06 11:06:17        cri

Majalisar dokokin Iraqi, ta amince da wani daftarin doka, dake bukatar gwamnati ta kori dakarun kasashen waje daga kasar, tare da hana su amfani da sararin samaniya da yankunanta na ruwa.

Yayin wata zama a jiya, 'yan majalisar masu rinjaye, sun kada kuri'ar amincewa da zartar da dokar dake bukatar gwamnati ta soke bukatar neman taimakon dakarun kawance wajen yaki da kungiyar IS, biyo bayan kawo karshen ayyukan soji da yaki a kasar.

Bisa matakin majalisar, ya kamata gwamnatin kasar ta kawo karshen kasancewar dakarun kasashen waje a yankunanta da kuma hana su amfani da sararin samaniyarta da yankunata na ruwa.

Baya ga haka, gwamnatin Iraqi, karkashin wakilcin ministanta na harkokin waje, ta shigar da korafi kan Amurka, bisa keta 'yancin kai da tsarin tsaron kasar.

Mai rikon mukamin Firaministan kasar, Abdel Abdul Mahdi, shi ma ya halarci zaman, inda ya gabatar da jawabi ga 'yan majalisar, yana mai cewa, ficewar dakarun Amurka daga Iraqi, za ta amfanawa kasashen biyu, musammam la'akari da abubuwan da suka faru a baya bayan nan. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China